Buhari ya yi ganawar sirri da takwaransa na Ghana a Abuja

Buhari ya yi ganawar sirri da takwaransa na Ghana a Abuja

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba, ya karbi bakuncin Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo

- Shugaba Buhari ya yi ganawar sirri da Akufo-Addo a Abuja

- Ana tsammanin ganawar zai kasance kan muzguna wa yan Najeriya da ake yi a kasar

Bayan sabanin da aka samu kan muzgunawar da ake yiwa yan Najeriya a Ghana, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da shugaba Nana Akufo-Addo.

An yi ganawar sirri tsakanin shugabannin na Afrika biyu a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, a daren ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba.

An sanar da batun ganawar tasu ne a shafin hadimin Shugaban kasar, Bashir Ahmad na Twitter.

KU KARANTA KUMA: Shugaban APC a Edo ya daura laifin nasarar da Obaseki yayi a PDP kan Oshiomhole

Buhari ya yi ganawar sirri da takwaransa na Ghana a Abuja
Buhari ya yi ganawar sirri da takwaransa na Ghana a Abuja Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Twitter

Koda dai babu wata sanarwa ta mahukunta game da ajandar ganawar tasu, baya rasa nasaba da halin da yan kasuwa na Najeriya da ke gana ke ciki da kuma kokarin ganin an samu alaka mai kyau tsakanin kasashen biyu da ke makwabtaka da juna.

Bayan labarin mummunan sabanin da ya shiga tsakani, ana iya cewa Ghana da Najeriya sun dau hanyar sulhu mai dorewa sakamakon ziyarar da kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya kai kasar.

Gbajabiamila wanda ya isa kasar mai makwabtaka a ranar Laraba, 2 ga watan Satumba, kan kudiri na diflomasiyya, ya gana da takwaransa na Ghana, Mike Oquaye.

Dan majalisar ya gana da wakilan yan kasuwa na Najeriya a Ghana wadanda suka sanar dashi halin da suka shiga a hannun jami’an gwamnatin.

KU KARANTA KUMA: Okorocha ya caccaki APC bayan PDP da Obaseki sun lashe zabe a Edo

A yayin zantawarsa da Oquaye, Gbajabiamila ya nuna yakinin cewa kasashen biyu na iya daukar matakan da za su kawo zaman lafiya da alaka mai kyau a tsakaninsu.

A wani labarin, mun kawo maku a baya cewa mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a ranar Talata ya wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron ECOWAS a Ghana.

Taron da ake gudanar da shi a Accra, babban birnin kasar, na daga cikin yunkurin shuwagabannin kasashen na kawo karshen rikicin kasar Mali.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel