Al’umma sun yi babban rashi – Sheikh Gumi ya yi martani kan mutuwar Sarkin Zazzau

Al’umma sun yi babban rashi – Sheikh Gumi ya yi martani kan mutuwar Sarkin Zazzau

- Sheikh Abubakar Gumi ya yi martani kan mutuwar Sarkin Zazzau

- Shehi Malamin ya mika ta’aziyyarsa a kan mutuwar Marigayi Shehu Idris

- Gumi ya bayyana mutuwar a matsayin babban rashi ga al’umma

Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi ya mika ta’aziyyarsa tare da alhini a kan mutuwar Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu a yau Lahadi, 20 ga watan Satumba.

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Facebook, Shehin Malamin ya bayyana mutuwar Basaraken a matsayin babban rashi ga al’ummah.

KU KARANTA KUMA: Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau

Ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai imani da son zaman lafiya.

Al’umma sun yi babban rashi – Sheikh Gumi ya yi martani kan mutuwar Sarkin Zazzau
Al’umma sun yi babban rashi – Sheikh Gumi ya yi martani kan mutuwar Sarkin Zazzau Hoto: Sheikh Abubakar Gumi
Source: Facebook

Gumi ya kuma yi masa addu’an samun afuwa da yafiyar Allah madaukakin Sarki.

Ya wallafa a shafin nasa: “Inna lillahi WA inna ilaihi rajiun! Mai martaba Sarkin Zazzau Alh. Dr. Shehu Idris ya kasance mutum mai imani da son zaman lafiya. Allah - Subhanahu Wa Taala- ya yafe masa sannan ya karbi kyawawan ayyukansa. Wannan babban rashi ne ga Al’ummah. Ina a hanyar zuwa wajen Janaizarsa. Rahmatullah alaihi. Amin."

KU KARANTA KUMA: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Marigayi Sarkin Zazzau

Da fari dai mun kawo maku cewa majiyoyi da dama da suke da kusanci da fadar sarkin sun tabbatar da rasuwarsa a yau Lahadi.

Marigayi Sarkin Zazzau shine Sarki na 18 na Fulani a masarautar Zazzau. Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Majiyoyi da dama sun tabbatar wa Legit.ng cewa, basaraken ya rasu a asibitin 44 da ke Kaduna wurin karfe 11 na safiyar Lahadi.

"Tabbas Allah ya yi wa Sarki rasuwa. Ya kwanta rashin lafiya tun a ranar Juma'a kuma an kai shi asibiti inda ya rasu.

"Nan babu dadewa za a dawo da gawarsa Zaria domin fara shirin jana'izarsa," wata majiya mai kusanci da Iyan Zazzau ta tabbatar.

Har ila yau mun kawo cewa da yammacin yau Lahadi, 20 ga watan Satumba ne gawar Marigayi Sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris ta isa Zaria, inda za a gudanar da jana'izarsa da misalin karfe biyar na yamma.

An gano dandazon jama’a da suka taru domin jana’izar marigayin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel