Babbar magana: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano za ta maka Sanusi kotu

Babbar magana: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano za ta maka Sanusi kotu

- Hukumar yaki da rashawa ta Kano za ta maka dakataccen sarkin Kano, Sanusi II a kotu

- Hukumar ta ba Sanusi kwanaki biyu ya amsa zarge-zargen da take masa

- Hakan na kunshe ne a cikin wata wasika da aka aikewa tsohon sarkin

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta ba tsohon sarki Kano, Muhammad Sanusi II, kwanaki biyu ya amsa zarge-zargen da ake masa.

Hukumar a watan Maris, ta bukaci Sanusi da ya gurfana a gabanta kan zargin siyar da wasu filaye a jihar ba bisa ka’ida ba.

A cikin wata wasika mai kwanan wata 8 ga Satumba, hukumar yaki da rashawar ta ce tana binciken: “yadda aka yi filayen da aka kebe a matsayin ‘Gandun Sarki’ wanda ya yadu a yankunan jihar da dama a karkashin shugabancin tsohon sarkin."

An tattaro cewa zargin da ake yiwa Sanusi na a kan sashi na 22, 23 da 26 na dokar jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

Babbar magana: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano za ta maka Sanusi kotu
Babbar magana: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano za ta maka Sanusi kotu Hoto: The Cable
Source: UGC

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Abubuwa 4 da ya kamata ku sani game da Gwamna Obaseki

“Bincike ya nuna cewa an yi cinikin siyar da kadarorin da ke mallakar masarautar ba bisa ka’ida ba tsakanin mutane uku wato Shehu Muhammad Dankadai (Sarkin Shehu), Sarki Abdullahi Ibrahim (Makaman Kano) da Mustapha Kawu Yahaya (Dan Isan Lapai) a madadin Ado Bayero Royal City Trust Fund kuma bisa umarnin ka.

“Wani lamari kuma dake bukatar karin haske daga gareka shine cewa a zama na hudu da aka yi a ranar 8 ga watan Yunin 2016, majalisar masarautar Kano ta amince da bukatar biyan kudi ga wani mashawarci (Messer Apple One Integrated Resources) kudi N175,000,990.90, amma sai ka umurci mutanen da aka ambata a sama da su biya kudin kai tsaye zuwa asusun masarautar sannan kamfanin da ke gudanar da aikin City Scape Properties Ltd. ta baiwa Dan Isan Lapai kudin biyan mashawarcin bisa umurninka da kuma wani N220 miliyan da wani abun da ba a sani ba.

“Har ila yau, kudin da kamfanin Countrywide House Ltd. ta biya na siyar da filayen Darmanawa Phase II ya kasance N225 miliyan, wanda daga ciki aka kwashe N266 miliyan a ranar 1 ga watan Agusta, 2018 zuwa asusun masarautar, wanda daga ciki aka bayar da umurnin tura N185,163,996.02 zuwa asusun Harara Turnkey Project Ltd. a ranar 7 ga watan Agustan 2018. Cewa daga cikin wannan kudin aka tura N147,590, 000 zuwa wani asusu mallakar wani Sani Hamisu Umar tsakanin 8-10 ga watan Agustan 2018, a rukuni hudu na N32 miliyan, N46 miliyan, N32 miliyan, N48 miliyan da kuma N3.590 miliyan.

“Hakazalika, a ranar 16 ga watan Disamba, 2016 an saka kudi N70, 0000,000 a asusun Turnkey Project Ltd. wanda aka kuma mayar dashi zuwa asusun kamfanin Majeeda Farms Ltd. duk a wannan rana. Wannan kamfani da ake magana a kai ana zargin cewa mallakinka ne kuma cewa kaninka, Mujitaba Abba ne ke kula da ita.

“Bincike ya kuma nuna cewa daga bisani an mayar da wadannan kudade zuwa asusunka na First Bank mai lamba 2666482899 lamari wanda yayi karo da sashi na 22 da 23 na dokar yaki da rashawa ta jihar Kano 2668. Misali. Sani Hamisu Umar ya tura N91,303,000 zuwa asusunka a ranar 25 ga watan Oktoba, 2018 a rukuni 10. Sannan a ranar 9 ga watan Nuwamban 2018, ya tura N2 1,500, 000 a rukuni uku zuwa asusunka.

“Wannan hukuma na ta jiran martaninka na amsa gayyatarmu bayan hukuncin da ke janye umurnin da babbar kotun tarayya ta bayar na wucin gadi inda ta umurci da bar komai yadda yake kan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Hotunan yadda dandazon jama'a suka cika wajen jana'izar Sarkin Zazzau

“Saboda haka hukumar na bin hanyar da ya dace na jin ta bakinka ta hanyar jan hankalinka kan ka mayar da martani ga zarge-zargen da ake maka a wannan wasikar sannan ka yi bayani dangane da lamarin, musamman alakarka da wadannan mutane da abun ya shafa.

“Muna sauraron martaninka kan lokaci da bai wuce ranakun aiki biyu ba daga lokacin da wannan wasika ya isa gareka.”

A wani labari na daban, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, Lamido Sanusi ya bayyana matsayarsa a kan karatun 'ya'ya mata wanda yace shine jigon cigaban kowacce al'umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel