Zaben Edo: Kada ka bayar da kai bori yah au, PDP ta roki shugaban INEC
- Jam'iyyar PDP ta roki shugaban INEC da kada ya bayar da kai bori ya hau kan matsin lambar da APC ke yi masa kan zaben gwamnan Edo
- PDP dai ta zargi APC da kokarin ganin an sauya sakamakon zabe saboda ta yi nasara
- Zuwa yanzu dai jam'iyyar PDP ke kan gaba bayan INEC ta kaddamar da sakamakon wasu kananan hukumomin jihar
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta zargi jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da matsa wa hukumar zabe mai zaman kanta canja sakamakon zaben gwamna a sassa daban-daban na jihar Edo.
A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, Kola Ologbondiyan, babban sakataren jam’iyyar na kasa, ya bukaci Mahmood Yakubu, Shugaban INEC, da kada ya amsa kiran domin hadin kai da zaman lafiyan kasar.
“Mun samu bayanan cewa Shugaban INEC na fuskantar matsin lamba daga APC domin ya bari a sauya sakamakon da aka kaddamar da yankunan ruwa na jihar Edo domin a karawa APC yawan kuri’u,” in ji sanarwar.
KU KARANTA KUMA: Sakamakon zaben gwamnan jihar Edo: APC na shan kaye
“Jam’iyyar PDP ta kuma lura cewa shafin INEC na yanar gizo na samun tangarda. Sannan muna da bayani kan shirin da ake na sauya sakamako a Fugar da sauran kananan hukumomi, duk a Edo ta arewa.
“Muna da sakamakon zaben da aka riga aka kaddamar a rumfar zabe daban-daban sannan muna bukatar INEC da ta tsare wadannan sakamako da jami’anta suka riga suka kaaddamar a rumfunan zabe.
“Muna gayyatan yan Najeriya da su sanya idanu sosai kan sakamkon da aka kaddamar a shafin yanar gizo na INEC domin tabbatar da ganin cewa ba a sauya muradin mutanen Edo a dare daya ba.
KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Oshiomole ya lallasa PDP a akwatinsa da tazara sama da 1200
A halin da ake ciki, jam'iyyar PDP ta sha gaban APC a yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke cigaba da sakin sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar Edo.
Hakan na nufin cewa dan takarar PDP kuma gwamnan jihar Edo mai ci, Godwin Obaseki, ya na kan gaba da rinjaye mai yawa a yayin da ake cigaba da sakin sakamakon zaben.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng