Kidayar Kuri'u: PDP ta sha gaban APC da banbancin kuri'a fiye da dubu 50

Kidayar Kuri'u: PDP ta sha gaban APC da banbancin kuri'a fiye da dubu 50

- Hukumar zabe ta kasa (INEC) ta fara sakin sakamakon zaben gwamnan jihar Edo bayan kammala kada kuri'a

- Ya zuwa duku-dukun safiyar ranar Lahadi, jam'iyyar PDP ce a kan gaba da tazara mai yawa

- Zaben kujerar gwamnan ya fi zafi a tsakanin gwamna mai ci, Godwin Obaseki, da babban abokin hamayyarsa, Osagie Ize-Iyamu, dan takarar APC

Jam'iyyar PDP ta sha gaban jam'iyyar APC a yayin da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) ke cigaba da sakin sakamakon zaben kujerar gwamnan jihar Edo.

Hakan na nufin cewa dan takarar jam'iyyar PDP kuma gwamnan jihar Edo mai ci, Godwin Obaseki, ya na kan gaba da rinjaye mai yawa a yayin da ake cigaba da sakin sakamakon zaben.

Ga wasu daga cikin sakamakon zaben kamar yadda INEC ta saki;

Karamar hukumar Igueben

PDP: 7,870

APC: 5,199

Karamar hukumar Esan central

PDP: 10,964

APC: 6,719

Karamar hukumar Esan north-east

PDP: 13,579

APC: 6,559

Karamar hukumar Esan south-east

PDP: 10,565

APC: 9,237

Karamar hukumar Ikpoba Okha

PDP: 41,030

APC: 18,218

Karamar hukumar Owan east

PDP: 14,762

APC: 19,295

Karamar hukumar Etsako west

PDP 17,959

APC 26,140

Karamar hukumar Egor

PDP: 27, 621

APC: 10, 202

Karamar hukumar Esan west

PDP – 17,433

APC – 7,189

Karamar hukumar Uhunmwonde

PDP: 10,022

APC: 5,972

Jimilla:

PDP: 171,805

APC: 114,730

Tazarar da ke tsakanin PDP da APC a halin yanzu: 57,075

Ana sauraron sakamakon zabe daga sauran kananan hukumomi 8.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng