Zaben Edo: Na karaya da hukumar INEC – Godwin Obaseki

Zaben Edo: Na karaya da hukumar INEC – Godwin Obaseki

- Gwamna Obaski ya nuna rashin jin dadi kan ayyukan hukumar INEC yayin zaben gwamnan jihar Edo

- Obaseki ya yi korafin cewa ya shafe fiye da awa daya a kan layi kafin ya samu jefa kuri'a saboda na'urar card reader da baya sauri

- Ya ce ya yi zaton hukumar zaben za ta yi shiri na musamman a wannan rana amma sai ya ga sabanin haka

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo, ya rashin jin dadi a kan yadda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ke gudanarwar da zaben gwamna a jihar.

Da yake magana da manema labarai bayan ya kada kuri’arsa a rumfar zabensa ta 019 da ke gunduma ta 4 a karamar hukumar Oredo da ke jihar, gwamnan ya ce ya shafe sama da sa’a daya a layi saboda rashin saurin na’urar ‘card reader’.

Obaseki ya ce ya yi tsammanin hukumar zaben za ta shiri na musamman, jaridar The Cable ta ruwaito.

Zaben Edo: Na karaya da hukumar INEC – Godwin Obaseki
Zaben Edo: Na karaya da hukumar INEC – Godwin Obaseki
Asali: Original

KU KARANTA KUMA: Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmad na shirin angwancewa da amaryarsa Naeema (hoto)

“Na yi tsammanin cewa INEC za ta yi shiri na musamman domin wannan zaben. Na tsaya kan layi tsawon awa daya da rabi kafin na samu damar kada kuri’ata, ban ji dadin lamarin ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa:“Kasancewar wannan rana ta zabe ce, ina ta tsammanin ganin shiri na musamman kan wannan zabe. Na’urar ‘card reader’ basu yi aiki cikin sauri yadda ya kamata ba kuma abun a koina ne.”

Da fari, Crusoe Osagie, mai ba gwamnan shawarar kan kafofin watsa labarai, ya yi zargin ceewa da gangan ake son kawo tangardar zabe a yankunan da Obaseki ya shahara.

“Kawai sai na’urar card reader suka daina aiki a yankunan da Gwamna Godwin Obaseki ya shahara sosai.

“An hana masu zabe isar da hakkinsu na kada kuri’a sannan muna iya cewa wannan makirci ne,” in ji shi a wani jawabi.

Da farko dai mun kawo maku cewa, al'ummar jihar Edo a yau Asabar, 19 ga watan Satumba, sun fara shirin zaben wanda zai rike ragamar mulkin jihar.

Akwai yan takaran kujeran gwamnan 14 dake fafatawa amma ana tunanin gwamnan da ke kai yanzu, Godwin Obaseki na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da Osagie Ize-Iyamu na All Progressives Congress (APC) ne wadanda zasu fafata.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: An harbi mutum daya a Edo

Alkaluman hukumar zabe INEC sun nuna cewa mutane milyan 1.72 ne zasu iya kada kuri'a yayinda 483,796 ba zasu iya ba saboda basu karbi katin zabensu ba.

Wakilan Legit.ng na jihar Edo yanzu haka domin kawo muku rahotanni kai tsaye game yadda abubuwa ke gudana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng