Mamba a majalisar wakilai ya koma APC bayan gwamnan PDP ya fada ma sa bakar magana

Mamba a majalisar wakilai ya koma APC bayan gwamnan PDP ya fada ma sa bakar magana

- Mamba a majalisar wakilai daga jihar Ribas, Chisom Dike, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC

- Honarabul Dike ya shaidawa manema labarai cewa ya mayarwa da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, kyautar motar alfarma da ya bashi

- A cewar dan majalisar, makiya sun shiga tsakaninsa da gwamna Wike har ta kai ga ba ya son su hadu sannan ya saka katangar karfe a tsakaninsu

Chisom Dike, mamba mai wakiltar maxabar Tai, Oyigbo, da Eleme a majalisar wakilai ya bar jam'iyyar PDP, ya koma jam'iyyar APC.

Yayin da ya ke tabbatar da komawarsa APC a gaban manema labarai, Dike ya bayyana cewa ya mayar da kyautar motar alfarma da gwamnan Ribas, Nyesom Wike, ya rabawa mambobin majalisar tarayya daga jihar.

Ya bayyana cewa ya zabi mayar da kyautar motar ne saboda yadda gwamnatin Wike ta yi watsi da matsalolin mutanen mazabarsa.

Dangane da dalilin komawarsa jam'iyyar APC, dan majalisar ya ce gwamna Wike ya ki yarda su gana domin tattauna matsalolin jama'arsa.

A cewar Dike, gwamna Wike ya matukar bashi mamaki yayin da ya fada masa cewa bai sanshi ba a lokacin da suka hadu.

KARANTA: Karin kuɗin wutar lantarki: Da sannu ƴan Nigeria za su gane amfanin hakan - FG

"Bani da ikon ganawa da gwamna domin tattauna matsalolin jama'ar da nake wakilta.

"Mun taba haduwa a baya, amma abin mamaki, sai ya ce bai sanni ba. Jin hakan ya matukar girgizani, saboda na bautawa jam'iyyar PDP tukuru lokacin yakin neman zabe.

"Shi (Wike) ya taka muhimmiyar rawa wajen samun tikitina na takara, na fahimci cewa bakar magana ya fada min kuma na fahimci sakonsa.

"Na tuntubi ma su ruwa da tsaki da magoya bayana kafin na yanke shawara. Ba ni da wani sauran amfani a PDP, dole na nemi kwanciyar hankali a wani wurin daban.

Mamba a majalisar wakilai ya koma APC bayan gwamnan PDP ya fada ma sa bakar magana
Nyesom Wike
Source: Facebook

"Ban taba samun kwanciyar hankali ba a jam'iyyar PDP, saboda sharrin makiya da ke zuga gwamna koda yaushe, hakan ne ma dalilinsa na kin yarda mu hadu," a cewar Dike.

KARANTA: Arangama tsakanin magoya baya: Rayuwata ake nema - dan takarar PDP a Ondo

A cewar Dike jama'ar da ya ke wakilta suna cikin mawuyacin hali saboda rashin kyawawan hanyoyin sufuri.

Dike ya kara da cewa akwai manyan jami'an gwamnatin jihar Ribas da suka fito daga mazabarsa amma sun gaza mayar da hankali wajen kawo cigaba a yankin.

"Babu hanyoyi ma su kyau a kananan hukumomin mazabata, tafiyar minti 30 za ta dauki mutum tsawon sa'a biyu saboda lalacewar hanyaoyin ababen hawa.

"Duk kokarina na son ganawa da gwamna domin tattauna matsalolin jama'a bai samu shiga ba, ba ya son ganina, ba ni da wani sauran amfani a wurinsa," a cewar dan majalisar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel