Mu na binciken kisan da aka yi a Garin Miyango inji ‘Yan Sanda
- An kashe wasu Ma’aurata yayin da su ke tafiya a kan babur
- Wannan lamarin ya auku ne a garin Miyago a Jihar Filato
- ‘Yan Sanda sun yi alkawarin gano wadanda su ka yi kisan
Dakarun ‘yan sandan Najeriya sun ce an harbe wasu ma’aurata a garin Miyango da ke karamar hukumar Bassa a Filato.
‘Yan sanda sun ce wasu miyagun ‘yan bindiga da ba a sansu ba ne su ka yi samame a cikin daji, su ka kashe ma’auratan.
Wannan lamari maras dadi ya faru ne a ranar Juma’ar da ta wuce da kimanin karfe 7:00 na yamma.
KU KARANTA: An cafke na-kusa da Yari da ake zargi ya na da alaka da 'Yan bindiga
Kakakin ‘yan sandan jihar Filato, Ubah Gabriel ya ce an zuba dakaru domin su binciko wadanda su ka yi wannan mugun aiki.
Wadannan Bayin Allah sun aukawa ajalinsu ne a lokacin da su ke shigowa cikin garin Miyango.
Kamar yadda jami’in ‘dan sandan ya bayyanawa ‘yan jarida, ana cigaba da bincike domin gano wadanda su ka yi laifin.
“Bincike ya na gudana da zai bayyana musababbin kisan da aka yi.” Ubah Gabriel.
KU KARANTA: Bauchi ta yi koyi da Kano, ta kawo BAROTA rage hadari
Mai magana da yawun ‘yan sanda, Ubah Gabriel, ya kara da cewa: “Za a hukunta wadanda su ka yi kisan.”
Daga lokacin da wannan abu ya faru a ranar 11 ga watan Satumba zuwa yanzu, ba a samu labarin nasarar kama ‘yan bindigan ba.
Wasu kungiyoyin Arewa sun fito sun ce kusohin gwamnati ke ba ƴan bindiga kariya. A cewar su, wasu manya a gwamnati ke daurewa 'yan bindiga gindi.
Ƙungiyoyin sun yi wannan jawabin ne game da zargin da su ke yi na cewa an saki wasu da ake zargin ƴan bindiga ne a Zamfara ba tare da bin ƙa'ida ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng