Tirkashi: Sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa sun fara gudun ceton rai akan kisan Gana a jihar Benue

Tirkashi: Sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa sun fara gudun ceton rai akan kisan Gana a jihar Benue

- Jama'ar jihar Benue suna cikin matsananciyar fargaba sakamakon kisan Gana da sojoji sukayi

- Ta kaiga wasu sarakunan gargajiya sun kwashe yanasu-yanasu sun gudu Makurdi saboda tsoron abinda zai je ya dawo

- Sannan kuma shuwagabannin kananan hukumomi suma basuyi kasa a guiwa ba wurin tserewa saboda tsoron yaran gagarumin dan ta'addarnan

A kwanakin baya ne sojoji suka kashe Tarwase Akwaza (Gana),shugaban 'yan ta'addan jihar Benue, hakan ya sanya wurare da dama da suka shiga cikin matsananciyar fargaba. Ta kaiga mazauna wuraren da suka hada da sarakunan gargajiya da kuma shuwagabannin kananan hukumomi duk sun shiga matsananciyar fargaba.

Tirkashi: Sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa sun fara gudun ceton rai akan kisan Gana a jihar Benue
Tirkashi: Sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa sun fara gudun ceton rai akan kisan Gana a jihar Benue
Asali: UGC

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito duka sarakunan gargajiya da shugabannin kananan hukumomi na garin Sankara sun tsere zuwa garin Makurdi, babban birnin jihar saboda tsoron kada a kawo musu farmaki.

Richard Gbande, wani dan majalisar wakilai ya bayyanar da tsoron barkewar rikici bayan shi da wasu shugabanni sunyi tattaunawar yadda aka kasheshi.

KU KARANTA: Kano: Matar aure ta shake dan kishiya, ya sheka lahira ko shurawa babu

Ya kara da cewa 'yan jarida da shugabannin gargajiyar Sankara da suka kama hanya takanas ta Kano domin raka Gana zuwa babban birnin jihar saboda ya ajiye makamanshi suma sun tsere.

Ya ce yanzu haka da yake magana da su Ter Ukum, Arc Orkar Kaave, Ter Logo, Jimmy Meeme, Ter Katsina Ala, har ma da Benjamin Fezanga Wombo sun bar gidajensu sun gudo Makurdi.

Duk wasu shuwagabannin kananan hukumomi sun gudu Makurdi. Babu wanda baya cikin fargaba yanzu haka.

KU KARANTA: Tun bayan fitowa ta a fim a matsayin El-Zakzaky ana yi mini barazanar kisa - Cewar jarumi Pete Edochie

Babu wani mai mulki ko kuma motar gwamnati da mutum zai gani a Sankara saboda tsoron da kowa yake ciki.

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom bukaci rundunar sojojin Najeriya ta saki ƴan daba guda 40 da suke tsare da su bayan kashe shugabansu Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana.

Gwamnan ya yi wannan kirar ne bayan taron tsaro da aka yi a gidan gwamnati a Makurdi na tsawon awa biyar a ranar Juma'a 11 ga watan Satumba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel