An cafke hadimin Gwamna Okowa da ya ɗauki hayar wasu su kashe wani ɗan kasuwa

An cafke hadimin Gwamna Okowa da ya ɗauki hayar wasu su kashe wani ɗan kasuwa

- 'Yan sanda daga Abuja sun kama hadimin gwamnan jihar Delta bisa zarginsa da hannu wurin yunkurin kashe wani dan kasuwa a Sapele

- Ana zargin cewa Sunday Okoro Ukwejemifor hadimin gwamna a kan tsaro ya ɗauki hayar wasu mutane domin su kashe ɗan kasuwa

- Kakakin 'yan sanda DSP Onovwakpoyeya ya tabbatar da kama Ukwejemifor da wasu mutane shida

An cafke hadimin Gwamna Okowa kan zargin yunkirin kisa
An cafke hadimin Gwamna Okowa kan zargin yunkirin kisa. Hoto daga The Nation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotuna: Wani mutum ya auri surukarsa bayan rabuwa da matarsa

Jami'ai daga hedkwatan 'yan sanda da ke birnin tarayya Abuja sun kama daya daga cikin hadiman gwamnan jihar Delta Ifeanyi Okowa a kan zargin yunkurin aikata kisan kai.

An ce wanda ake zargin, Sunday Okoro Ukwejemifor yana da hannu cikin yunkurin kashe wani dan kasuwa a garin Sapele mai suna Sunny Nwakego.

DUBA WANNAN: Hotuna: Dan majalisar Najeriya sai aurar da ƴaƴansa 5 a rana ɗaya

The Nation ta ruwaito cewa Ukwejemifor, mataimaki na musamman ga gwamna Okowa a kan tsaro ya dade 'yan sanda na sa ido a kansa tun a shekarar 2009 kan zarginsa da hannu a garkuwa da mutane, fashi, kisan kai da kone-kone.

An kama shi tare da wasu mutane shida da ake zarginsu da hannu wurin yunkurin kisar.

Ana zargin cewa Ukwejemifor ya dauki hayar wasu mutane biyar daga Fatakwal, Jihar Rivers su kashe dan kasuwan.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda, DSP Onovwakpoyeya ya tabbatar da kama wadanda ake zargin.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, jami'an tsaro a kasar Uganda sun bazama neman wasu fursunoni fiye da 200 da suka tsere daga gidan yari, sun shiga wurin ajiye makamai sun tube tufafinsu sannan suka bazama cikin daji a arewa maso gabashin kasar.

A kalla mutane uku - daya soja biyu kuma cikin fursunonin - sun rasa rayyukansu yayin musayar wuta da aka yi a cewar kakakin rundunar sojin kasar, Birgediya Flavia Byekwaso.

Fursunonin sun tsere daga gidan yarin ne a ranar Laraba kusa da barikin sojoji da ke Moroto. "Sun ci galaba a kan direbobin da ke aiki a ranar," in jiBirgediya Flavia Byekwaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel