Farfesa Sagay ya yi kaca-kaca da sabon kudirin durkusar da aikin Jami’an EFCC
- Itse Sagay ya yi Allah-wadai da sabon kudirin da zai rage karfin EFCC
- Masanin shari’ar ya kira wadanda su ka kawo kudirin ‘Makiyan kasa’
- Hadimin Shugaban kasar ya bada shawarar ka da a yarda da kudirin
Kwamitin da ke ba shugaban Najeriya shawara kan harkar barayi da rashin gaskiya, PACAC, ta yi magana a kan shirin kafa sabuwar hukumar yaki da barayi.
Shugaban PACAC, Farfesa Itse Sagay, ya soki shirin yi wa dokar EFCC kwaskwarima da kuma kirkiro wata sabuwar hukumar da za ta durkusar da aikinta.
Farfesa Itse Sagay ya bukaci mutanen Najeriya da ‘yan majalisa su ki amincewa da wannan doka.
Sagay a jawabin da ya fitar a matsayinsa na shugaban PACAC, ya ce wadanda su ka shirya kudirin, su na jin kunyar kansu, don haka su ka boye sunayensu.
KU KARANTA: Rikicin kungiyar NBA ta sa Lauya ya shigar da karar Ministan shari’a
Wannan jawabi ya fito ne daga ofishin sadarwa na kwamitin PACAC a ranar Alhamis. Kwamitin ya ce kudirin da aka kawo ya na hadari kuma zai kao cikas.
Yakin da ake yi da barayi zai koma kamar yadda aka sani kafin 2015 inji PACAC. Kwamitin ya ce wakilan barayin kasar nan ne su ka shigo da wannan kudiri.
Sagay ya ce: “Kudirin na neman karya EFCC da jami’anta, sannan a daura iko mai nauyi na hukumar a ofishin ministan shari’a, kuma babban lauyan gwamnati.”
Duk da haka, Sagay bai furta cewa minista Abubakar Malami ne ya haifi wannan kudirin ba.
KU KARANTA: Manyan Gwamnati su na da hannu a kashe-kashen da ake yi
Ya ce: “Za a cire karfin ikon da aka ba EFCC, a maida ta hukuma a karkashin ma’aikatar shari’a.”
“Da wadannan bayanai, barnar da canjin za ta yi, ya na da matukar yawa.” Sagay ya ce musamman idan aka duba yadda AGF ke hana binciken wasu da ake zargi.
“Don haka mu na kira ga majalisar tarayya da ‘yan Najeriya su nuna rashin goyo baya ga wannan shirin barna da ake yi na kawo karshen yaki da barayi da toshe EFCC.”
Dazu kun ji cewa kamar yadda Ibrahim Magu ya taba fada, Sagay SAN ya ce Ministan shari’a ya na shinge wadanda ake zargi da manyan laifuffuka a Najeriya.
Sagay ya ce ana amfani da ofishin AGF wajen fatali da shari'ar wasu na kusa da masu mulki.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng