Sagay ya zargi Malami da watsi da binciken manyan wadanda ake zargi da laifi
- Itse Sagay SAN ya ce Ministan shari’a ya na kin binciken wasu manya
- Hadimin Buhari ya ce Malami ya kan hana a taba wasu da ake tuhuma
- Farfesan bai fito ya kama sunayen wadanda Ministan ya katangen ba
Itse Sagay ya zargi ministan shari’a, Abubakar Malami, da laifin watsi da wasu bincike masu nauyi da ake yi a kan manyan wadanda ake zargi a Najeriya.
Farfesa Itse Sagay ya ce babban lauyan gwamnatin tarayyar ya yi suna wajen birne bincike da ake yi a kan wasu jami’an gwamnati da fitattun ‘yan siyasa.
Sagay ya yi wannan jawabi ne a jiya a madadin majalisar PACAC mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara game da harkar rashin gaskiya.
KU KARANTA: Abubakar Malami ya ke hana a binciki masu laifi - Lauya
Masanin harkar shari’ar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya ke sukar wani sabon kudiri da gwamnati ta shigo da shi da zai ragewa hukumar EFCC karfi.
Jaridar Premium Times ta ce ministan bai maida martani game da wannan zargi mai nauyi ba.
‘Yan jarida sun tuntubi hadimin ministan, Dr. Umar Gwandu, amma ya ki daukar waya, sannan bai bada amsar sakonnin da aka aika masa a ranar Laraba ba.
KU KARANTA: Malami: Magu ya yi karin haske kan zargin da ake yi masa
Itse Sagay bai kama sunayen wadanda ake zargin Abubakar Malami da kin bincikensu ba, amma ba wannan ne karon farko da aka yi wa ministan wannan shaida ba.
Tun 2017 ake jita-jitar ana amfani da ofishin AGF wajen watsi da binciken da hukumar EFCC ta ke yi a kan wasu da ake zarginsu da laifin cin kudin gwamnati.
Daga cikin misalan da Magu ya bada a wata takarda, ya ce akwai wani tsohon shugaban banki da tsohon ministan da minista ya sa aka dakatar da bincikensu.
Ibrahim Magu ya na zargin AGF ne ya kawo cikas wajen binciken Diezani Alison-Madueke.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng