Quique Setien zai yi karar Barcelona, ya nemi a biya shi fam €4m - Lauya
- Quique Setien ya fito ya yi jawabi bayan Kungiyar Barcelona ta kore shi
- Kocin zai shigar da kara a kan kulob din, ya bukaci a biya shi wasu kudi
- Barcelona ta maye gurbin Setien da Koeman bayan an doke ta 8-2 a UCL
Quique Setien ya tabbatar da cewa zai kai karar kungiyar Barcelona a kotu ganin cewa sai ranar Larabar nan aka sanar da shi an sallame shi daga aiki.
Kungiyar Barcelona ta karkare ban-kwana da Quique Setien ne a cikin makon nan, bayan wata guda da Barcelona ta sanar da cewa ta raba gari da shi.
Punch ta ce Lauyoyin Quique Setien za su kai lamarin ga Alkali, inda za su nemi kungiyar kwallon kafan ta biya kocin fam miliyan €4 a matsayin alhaki.
KU KARANTA: Wanene sabon Kocin Barcelona, Quique Setien?
Jawabin da Setien ya fitar ya tabbatar da cewa sai a ranar 16 ga watan Satumba ne labari ya kai gare shi cewa kungiyar Barcelona ta kore shi daga aiki.
Haka zalika a tsakiyar wannan makon nan ne ma’aikatan tsohon kocin su ka samu takarda daga kulob, inda aka sanar da su cewa za a sauya masu wurin aiki.
Quique Setien mai shekaru 61 ya buga wasansa na karshe a matsayin koci ne a watan Agusta.
A watan Junairun shekarar nan Barcelona ta dauko hayar Quique Setien bayan ta sallami Ernesto Velverde, da nufin cewa abubuwa za su sake zani a kulob din.
KU KARANTA: Barcelona ta dauko hayar Koeman ya maye gurbin Setien
Bayan watanni bakwai ya na aiki a matsayin mai horas da ‘yan wasa, Barcelona ta bada sanarwar datse yarjejeniyarta da Setien wanda ya kamata ya kai 2022.
Rahotannin da su ke fitowa sun nuna cewa Barcelona ta sauke Setien ne daga matsayin kocinta, amma har yanzu ya na da kwantiragi tare da kungiyar ta Sifen.
Idan za ku tuna tun a kwanakin baya Barcelona ta fitar da jawabi cewa Quique Setien ya tashi daga matsayin mai horas da manyan ‘yan wasan kwallon kafanta.
Barcelona ta dauki wannan mataki ne sakamakon mummunan kashin da ta sha a hannun kungiyar Jamus, Bayern Munich a gasar zakarun Nahiyar kofin Turai.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng