Zaben Edo: APC za ta kwashi kashinta a hannu idan aka cire ƴan bangar siyasa - Wike
- Gwamna Nyesom Wike ya yi hasashen sakamakon zaben Edo
- INEC za ta gudanar da zaben gwamna a jihar a ranar Asabar, 19 ga watan Satumba
- Wike ya ce APC za ta sha gagarumin kaye idan aka hana ta amfani da yan bangan siyasa
Kasa da sa’o’i arba’in da takwas kafin gudanar da zaben gwamnan Edo, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya yi hasashen sakamakon zaben.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa gwamnan ya ce idan har yan sanda suka yi nasarar hana yan daba taka rawar gani a yayin zaben gwamnan, toh jam’iyyar All Progressives Congress (APC) za ta kwashi kashinta a hannu.
Legit.ng ta tattaro cewa yayinda yake magana a wata hira a tashar African Independent Television (AIT) a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumba, Wike ya ce dama guda da APC ke dashi na yin nasara shine ta hanyar “yin magudi a tsarin.”
Ya kuma bukaci mutanen jihar da su zauna lafiya sannan su kare tsarin zaben.
KU KARANTA KUMA: APC ta yi babban rashi: Tsohon gwamnan Adamawa ya sanar da ficewarsa, ya koma PDP
“Sufeto Janar na yan sanda ya ce ba za su bayar da kowani dama ga yan daba ba, kuma addu’armu ce ganin an yi hakan idan aka aikata hakan, APC za ta kwashi kashinta a hannu. Idan aka aiwatar da abunda IG yace, za ku ga cewa ko kusa APC ba za ta kai ba – dama guda da suke dashi shine taa hanyar amfani da hukumomin tsaro.
“Ku tuna abunda ya faru a kaina sannan idan kuka dauki lamarin jihar Ribas, a bayyane yake karara, sannan a yadda nake kallon APC, ta kagu sosai kuma dama guda da APC ke dashi a yau shine amfani da jami’an tsaro, domin tayi magudi a tsarin.
“Damuwarmu shine mu bari mutanenmu su san cewa, idan yan sanda suka bayar da kai bori yah au, ba zamu bari ba. Muna so mu yarda dasu amma, kada kuyi kasa a gwiwa, ku tabbatar kun kafa-kafa dasu.
“Ku tabbatar kun zuba idanu kan abunda ke faruwa. Kada ku bari wani dan sanda yace maku ba za ku iya bin sakamakon zabe zuwa wajen tattara kuri’u ba bayan an kaddamar da sakamako a wajen zabe,” in ji shi.
KU KARANTA KUMA: Hotuna: INEC ta kai kayayyakin bukata na zaben jihar Edo
Gwamnan na Ribas ya ce Godwin Obaseki ya yi kokari sosai wajen nagartaccen shugabanci.
A gefe guda, wani jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Cif Sam Nkire, ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa.
Jaridar The Sun ta ruwaito cewa Nkire wanda ya kasance mamba a kungiyar masu ruwa da tsaki na APC ta kasa, ya ce nasarar na iya zama gab da gab, inda ya kara da cewa ‘nasara sunansa nasara.'
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng