Hotuna: INEC ta kai kayayyakin bukata na zaben jihar Edo
- Kusan sa'o'i 48 da suka rage kafin zaben gwamnan jihar Edo, INEC ta kai kayayyakin bukata
- Kamar yadda hotunan suka bayyana, jami'an tsaro sun cika makil don bada kariyar da ta dace
- An ajiye kayayyakin zaben ne a babban bankin Najeriya amma reshen jihar Edo a Benin City
Kasa da sa'o'i 48 zuwa zaben gwamnoni na jihar Edo, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fara kai kayayyakin bukata na zaben jihar.
Gidan talabijin na Channels ya gano cewa, an ajiya kayayyaki masu matukar amfani na zaben a babban bankin Najeriya reshen jihar Edo da ke Benin City, inda suke ajiye kafin a fara rarrabewa.
An ga jami'an tsaro sun cika wurin daga rundunar sojin Najeriya, 'yan sanda da sauransu.
KU KARANTA: Boko Haram: Dahiru Bauchi, ya musanta goyon bayan Mailafia a kan ikirarinsa
KU KARANTA: Cutata aka yi, ashe tana da 'ya'ya uku na aureta - Magidanci ya sanar da kotu
A wani labari na daban, tsohon ministan harkokin waje, Tom Ikimi, ya sanar da babban jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu, cewa motocin da ke dankare da kudi a cikin gidansa ba za su iya siyan kujerar gwamnan jihar Edo ba a zaben da ke zuwa a ranar Asabar.
Ikimi ya sanar da hakan a gagarumin gangamin siyasa da 'yan jam'iyyar PDP suka fito a babban birnin jihar Edo a ranar Talata.
Tsohon ministan ya sanar da hakan ne yayin martani ga wani bidiyo wanda Tinubu yake kira ga jama'ar jihar Edo da kada su kuskura su zabi Obaseki.
A yayin martani ga bidiyon, Ikimi, wanda a da babban jigo ne a jam'iyyar APC, ya ce Tinubu bashi da wata dukiya a 1999 kafin ya hau kujerar gwamnan jihar Legas.
A don haka ya yi kira ga Tinubu da ya bayyana wa 'yan Najeriya tushen dukiyarsa.
Tsohon ministan, yayin magana a kan motocin kudin da aka gani a harabar gidan Tinubu a kusa da zaben 2019, ya ce ba zai yuwu a siya jihar Edo ba, kuma ya ja kunnen Tinubu da ya kiyayi jihar.
Ikimi ya ce bidiyon Tinubu wata babbar shaida ce da ke nuna cewa zaben ba tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da Fasto Osagie Ize-Iyamu bane kadai.
A maimakon hakan, zaben tsakanin Obaseki ne da Tinubu tare da Adams Oshiomhole.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng