Monday Ubani ya na karar Abubakar Malami kan ‘yunkurin karya NBA’

Monday Ubani ya na karar Abubakar Malami kan ‘yunkurin karya NBA’

- Monday Ubani ya shigar da kara a kan Abubakar Malami SAN a kotu

- Lauyan ya na so a ruguza matakin da Ministan ya dauka game da NBA

- Ubani ya riga Falana kai Malami kotu a kan zargin durkusa kungiyarsu

Domin nuna bore, wasu lauyoyi sun sa hannu a wata takardar korafi, su na neman a tsige Abubakar Malami daga mukamin SAN na babban lauya.

Lamarin har ya kai ga wani Lauya mai suna Monday Ubani ya kai maganar gaban kuliya, ya na neman a fayyace masa sabanin da ya shiga tsakaninsu da AGF.

Monday Ubani ya tunkari Alkali ne domin jin ko ministan shari’a ya na da ikon da zai taba dokokin kungiyar lauyoyi ba tare da amincewar majalisar sharia’a ba.

Jaridar Punch ta ce Ubani ya na kokwanton karfin ikon Abubakar Malami ta yadda ya dauki hukunci a hannunsa ba tare da jin ta sauran bakin masu ta-cewa ba.

KU KARANTA: Falana ya nemi Gwamnatin Buhari ta saki su El-Zakzaky

Lauyan ya na ikirarin cewa sashe na 12(4) na dokokin shari’a da Malami ya dogara da su, ba su ba shi cikakken hurumin da zai sauya dokokin irinsu NBA ba.

Asali ma, Ubani ya na ganin akasin haka, ya ce sashe 1 da 12 na dokar ta daurawa majalisar da ke da alhakin rantsar da sabbabin lauyoyi wannan nauyi ne.

Monday Ubani ya na karar Abubakar Malami kan ‘yunkurin karya NBA’
Ministan shari'a Abubakar Malami SAN
Asali: Twitter

Wannan majalisa ta na dauke da Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, da kuma wasu mutane 20 daga cikin kungiyar lauyoyi na kasa.

A dalilin wadannan hujjoji, Lauyan ya roki Alkali ya bayyana kwaskwarimar da Malami ya yi wa dokokin kasa a matsayin wadanda su ka ci karo da tsarin mulki.

KU KARANTA: Hawa jirgin shugaban kasa da Hannan ta yi haramun ne - SAN

Monday Ubani ya kuma bukaci a rusa sashe na 23A na wannan doka ta kungiyar masana harkar shari’a, wanda ta hana a shigar da kara game da sha’anin NBA.

Kawo yanzu ba mu samu labarin yaushe Alkali zai zauna a kan wannan shari’a ba.

A baya kun ji yadda wasu gungun Lauyoyi su ka huro wuta a cirewa Ministan shari'a, Abubakar Malami mukamin ‘SAN’ saboda zarginsa da ake yi da kassara NBA.

Lauyoyi fiye da 300 su ka sa hannu domin a raba Ministan da mukamin SAN

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel