Tashin hankali: Mayaƙan Boko Haram sun kai hari Borno, sun kashe mutane 10

Tashin hankali: Mayaƙan Boko Haram sun kai hari Borno, sun kashe mutane 10

- Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan ababen hawa sannan suka sace mutane da dama dake ciki a Borno jihar

- An tattaro cewa yan ta'addan sun kashe kimanin mutum 10 daga cikinsu

- Har ila yau rahoton ya nuna cewa yan ta'addan sun kai kimanin su 30

Yan ta'addan Boko Haram sun kai hari a jihar Borno, sun kashe kimanin mutum 10 sannan suka sace wasu da dama.

Lamarin ya afku ne da misalin karfe 7:00 na yamma a kauyen Wassaram, unguwar Ngamdu da ke karamar hukumar Kaga na jihar, jaridar Daiy Trust ta ruwaito.

Jaridar ta ce mutanen da lamarin ya cika dasu duk fasinjoji ne wadanda suka ajiye motocinsu a hanyar sakamakon hana ababen hawa zirga-zirga da aka yi da yamma.

Tashin hankali: Mayaƙan Boko Haram sun kai hari Borno, sun kashe mutane 10
Tashin hankali: Mayaƙan Boko Haram sun kai hari Borno, sun kashe mutane 10 Hoto: Hudson Institute/Thisday
Source: Twitter

Wata majiya tace mutane da dama sun jikkata yayinda maharan suka yi garkuwa da fasinjoji da yawa.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: Babban jigon APC ya yi hasashen nasara ga jam’iyyarsa

"Boko Haram sun zo kauyen Wassaram da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Talata. Jim kadan bayan mun gama sallar dare. Kimanin su 30 sannan sun zo a cikin motoci uku. Sun hadu da wasu mutane yayinda suke shiga kauyen.

"Sun sanar da mazauna wajen cewa su bar wajen domin wasu mutane na hanyar kawo masu hari. Don haka sai mutane suka fara gudu kuma abunda basu sani ba wadannan mutane na motoci ukun yan Boko Haram ne. Sai suka fara harbinsu. Sun kashe mutum 10, da dama sun jikkata.

"Na ga gawarwaki," in ji wata majiya ta yan banga.

Wani idon shaida, Ali Saleh, ya ce mazauna yan kin da dama sun tsere cikin jeji.

"Har yanzu ba a ga wasu matafiya da dama ba," in ji shi.

Hakazalika wani dan bangar CJTF, Mustapha Usman, ya ce harin ya kai kimanin sa'a guda yana gudana.

"Sun ci karensu babu babbaka. Babu wanda ya taka masu birki daga koina. Da fari, mun ga gawarwaki takwas a wajen, amma da maraicen jiya sai aka sake gano gawarwaki biyu a cikin motocin. Sun kona fiye da gidaje 10, yayinda mutane da dama suka tsere da raunuka.

"Sun tafi da wasu fasinjoji wadanda basu san kan yankin ba," in ji Usman.

KU KARANTA KUMA: Abinda yasa muka kama jigon jam'iyyar APC a Zamfara - 'Yan sanda

A wani labarin, gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya ta ce yan ta'adda da yan bindiga na cin karnukansu ba babbaka kulli yaumin a Arewa maso gabas da yamma.

A hira da manema labarai, kakakin gamayyar, Abdul-Aziz Suleiman ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta tashi tsaye wajen dakile yan bindigan da masu daukan nauyinsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel