Yadda wani biri ya saci wayar wani mutumi yaje ya dinga daukar hoto da bidiyo da ita

Yadda wani biri ya saci wayar wani mutumi yaje ya dinga daukar hoto da bidiyo da ita

- Wani biri ya shiga wani gida a kasar Malaysia, inda ya sunkuce waya yayi kokarin cinyeta ya arce cikin daji da ita

- Wayar ta wani mutumine dan kasar Malaysia mai shekaru 20 da haihuwa, daga baya aka tsince ta cike da hotuna da bidiyoyin birai makil

- Birin ya sace wayar ne a ranar Asabar 12 ga watan Satumba, kuma an tsinceta ne washegari bayan dabbobin sun fahimci batada wani amfani a garesu

Wani mutumi dan Malaysia mai suna Zackrydz Rodzi ya tsinci wayarsa cike da hotuna da bidiyoyin birai bayan da wani biri ya sace mishi wayar.

Mutumin mai shekaru 20 da haihuwa ya sanar da BBC cewa bayan ya tashi daga bacci da misalin karfe 11 na safiyar ranar Asabar 12 ga watan Satumba, ya nemi wayarsa sama da kasa ya rasa. Sai dai daga baya ya tsinceta a wani wuri daban cike da hotuna da bidiyo na birai.

Yadda wani biri ya saci wayar wani mutumi yaje ya dinga daukar hoto da bidiyo da ita
Birin ya bar bidiyon shi da hoton shi a cikin wayar da ya sace | Photo Credit: Zackrydz Rodzi
Source: UGC

A cikin bidiyon da ya gani a wayar tasa, yaga lokacin da birin ke kokarin cinye wayar. An tsinci wayar ne a karkashin ganyayyaki a kasan wata bishiyar kwakwa bayan Rodzi ya kira wayar yaji kararta a wurin.

KU KARANTA: An bawa wata budurwa marainiya da bata da hannu kyautar wani kyakkyawan gida mai dakuna uku

Mutumin yace babu wata alamar fashewa a jikin wayar. Birin da ake zargi ya shiga dakin shine ta tagar kaninshi da take a bude.

Ya ce: "banga alamar fashi ba. Kawai nayi tunanin anyi amfani da wani irin tsafi ne." Da ya kira wayar yaji kararta ne a cikin wani daji da yake bayan gidansu.

Yace ya tsinci wayar duk tasha 'kura a kasan wata bishiyar kwakwa.

KU KARANTA: Mutumin da yake acaba yana biyawa kanshi kudin makaranta ya zama dalibin da yafi kowa sakamako mai kyau

Shi kuma wani mutumi a wani bidiyo da yake ta yawo, ya nuna lokacin da wata katuwar giwa ta kai mishi hari a lokacin da yake tafiya akan keke, ta kayar da shi sannan ta kwace keken.

A bidiyon, mutumin dake tuka keken an ganshi kwance a kasa kusa da keken nashi, yayin da ita kuma giwar ta tsaya a kanshi.

Mutumin wanda alamu na nuni da cewa ya tsorata. bai gudu ba, maimakon haka sai ya kwanta a wajen.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel