Hujja ta yi ɓatan dabo: An samu tarnaƙi a shari'ar Fatima da Atiku Abubakar

Hujja ta yi ɓatan dabo: An samu tarnaƙi a shari'ar Fatima da Atiku Abubakar

- An shiga kotu domin sauraron shari'a tsakanin dan Atiku Abubakar da tsohuwar matarsa da ya saka, Maryam Sheriff

- Maryam dai ta shigar da kara inda take rokon kotu da ta mika mata ragamar kula da yaransu guda uku

- Sai dai an samu tsaico domin lauyan wanda ake kara bai bayyana a kotu ba domin gabatar da hujja ta karshe

Yayinda aka dawo zaman domin sauraron karar da Maryam Sheriff, matar da Alhaji Atiku Abubakar ya saka ta shigar na son a mallaka mata ragamar kula da yaransu a ranar Laraba a babbar kotun Kubwa, Abuja, wanda ake kara ya gaza gabatar da shaidarsa ta karshe.

Abubakar ya kasance da ga tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma sunansu iri guda.

Sherif ta shigar da kara a kan Abubakar a babbar kotu da ke Gudu, Abuja, amma sai aka tura lamarin zuwa babban kotu da ke Kubwa.

Ta roki kotu da ta bata damar ci gaba da kula da yaransu maza su uku, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Zaben edo: NSCDC ta tura jami’ai 13,311 da karnukan farauta 60

Hujja ta yi ɓatan dabo: An samu tarnaƙi a shari'ar Fatima da Atiku Abubakar
Hujja ta yi ɓatan dabo: An samu tarnaƙi a shari'ar Fatima da Atiku Abubakar
Source: Getty Images

Da aka dawo zama kan lamarin a ranar Laraba, lauyan da ke kare wanda ake kara, Abdullahi Hassan, bai halarci zaman kotun ba amma sai ya turo Isah Suleiman dauke da wata wasika zuwa ga kotun.

A cikin wasikar ya bayyana cewa ba zai samu zuwa ba saboda ya rasa wani kawunsa kuma ya tafi jana’izarsa.

A wasikar wacce aka karanta a gaban kotun, Hassan ya bukaci kotun da ta dage zaman zuwa ranar 7 ga watan Oktoba, 2020.

Ya kamata lauyan ya gabatar da shaida a kotun, sakamakon rashin gabatar dashi a zaman da aka yi a baya saboda sun ce shaidan na kasar Dubai.

Lauyan mai kara, Nasir Saidu, ya bukaci kotun da ta yi watsi da wasikar sannan ta bari ya yi jawabi a gabanta bisa doka domin a yanke hukunci kan lamarin.

Saidu ya ce wasikar bai da wani fa’ida kuma cewa shiri ne na son kawo tsaiko a lamarin.

KU KARANTA KUMA: Mayaƙan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, mutane 8 sun mutu

Alkalin, Justis Bashir Dansule, ya yi watsi da bukatar lauyan wanda ake kara sannan ya dage zaman zuwa ranar 22 ga watan Satumba domin ci gaba da shari’a.

Ya umurci lauyan wanda ake kara da su gabatar da shaidarsu na karshe a kotu ko kuma a zartar da bukatar lauyan mai kara.

A wani labarin, wani mai walda da ke zama a Ibadan mai suna Quozeem Owolabi, ya maka matarsa Tunrayo a gaban wata kotun gargajiya da ke zama a Ile-Tuntun, Ibadan, jihar Oyo.

Ya bukaci da a tsinke igiyar aurensu mai shekara daya a kan abinda ya kwatanta da rufa-rufa. Ta ki sanar masa cewa tana da 'ya'ya har uku kafin su yi aure.

Bugu da kari, Owolabi ya yi korafin cewa bata sallah da azumin watan Ramadana, kamar yadda ta yi masa alkawari kafin su yi aure.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Online view pixel