‘Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ya na shirin komawa kungiyar Tottenham

‘Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ya na shirin komawa kungiyar Tottenham

- Gareth Bale ya kusa kammala komawa bugawa kungiyar Tottenham wasa

- ‘Dan wasan gaban zai hadu da Jose Mourinho a tsohon kulob din da ya bari

- Bale ya tashi daga Tottenham zuwa Real Madrid ne a kakar shekarar 2013

Sky Sports ta bayyana cewa maganar komawa Gareth Bale Tottenham ta yi nisa, har ta kai ‘dan wasan ya na jiran lokaci ne kurum ya tashi daga Real Madrid.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Gareth Bale ya na jiran amincewar kungiyar Real Madrid ne domin ya hau jirgi ya tafi Landan, inda zai zauna da Tottenham.

Dillalin ‘dan wasan gaban na kasar Wales, ya shaidawa Sky Sports News cewa ba a taba yin lokacin da Bale ya ke gab da tashi daga Real Madrid ba kamar yanzu.

KU KARANTA: Bale ya bar tarihi a gasar cin kofin Turai

Gareth Bale mai shekara 28 zai hau jirginsa daga Madrid ya wuce Arewacin Landan, inda zai rattaba hannu a kwantiragin Tottenham, kulob din da ya baro.

Tattaunawa tsakanin kungiyoyin biyu ta yi nisa, inda lauyoyin kowane bangare su ka zo daf da samun yarjejeniya a ranar Laraba, 16 ga watan Satumba, 2020.

Jaridar Daily Mail ta na ganin cewa kusan Gareth Bale ya zama ‘dan wasan Tottenham bayan Jose Mourinho ya fito ya nuna sha’awar da ya ke yi wa ‘dan wasan.

Bale ya samu kansa cikin wani mawuyacin hali a Real Madrid bayan kungiyar ta biya kudin da su ka fi kowane yawa sa’ilin da ta saye shi shekaru bakwai da su ka wuce.

KU KARANTA: Ina makomar Bale a Real Madrid?

‘Dan wasan Real Madrid, Gareth Bale ya na shirin komawa kungiyar Tottenham
Mourinho ya na neman cika burinsa na sayen Gareth Bale
Asali: Facebook

Tottenham ta dauko hayar Mourinho ne a shekarar bara da sa ran cewa abubuwa za su sake zani a White Hart Lane. Kocin ya gamsar da Daniel Levy game da bukatar Bale.

Idan an karkare magana, Bale zai sa hannu a kwantiragi mai tsawo da Tottenham. Hakan zai kawo karshen rade-radin da ake yi na cewa Manchester United ta na nemansa.

Tun a bara ku ka ji cewa Real Madrid ta na neman yadda za tayi da Gareth Bale a dalilin zama ala-ka-kai da ya yi wa kulob din, ya na cin albashi, amma ba ya buga wasa.

Har ta kai ana rade-radin shugaban kungiyar Real Madrid ya na neman sakin Gareth Bale, ya sayo 'dan wasan NajeriyaSamuel Chukwueze da ke bugawa kungiyar Villarreal.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel