Yadda faston mu ya yaudare ni ya kai ni Rasha karuwanci - Budurwa

Yadda faston mu ya yaudare ni ya kai ni Rasha karuwanci - Budurwa

- Florence Abu, wata budurwa ƴar asalin jihar Edo ta bayyana yadda faston cocin su ya yaudare ta ya kai ta karuwanci ƙasar waje

- Florence ta ce kafin tafiyar ta ya faɗa mata cewa ubangiji ya nuna masa cewa arzikin ta na ƙasar waje ne

- Amma tana isa ƙasar Rasha sai ta gano cewa karuwanci za ta yi ba aiki ba kuma ta sha baƙar wahala

Wata budurwa, Florence Abu, mai sana'ar gyaran gashi ta magantu kan yadda faston cocinsu ya yaudare ta ya kai ta Rasha karuwanci a shekarar 2012.

Ta yi tsamanin za ta tafi ƙasar wajen neman arziki ne kamar yadda wasu ƴan Najeriya ke zuwa wasu ƙasashen waje aiki.

Florence, ƴar asalin jihar Edo ta ce bayan isar ta Rasha ne ta gano cewa ashe karuwanci aka kai ta yi.

Faston mu ya yaudare ni ya kai ni Rasha karuwanci - Budurwa
Faston mu ya yaudare ni ya kai ni Rasha karuwanci - Budurwa. Hoto daga Premium Times
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun kashe mahaifi, sun yi awon gaba da ɗansa a Katsina

Ta yi ikirarin cewa wani Endurance Ehioze, mataimakin fasto a Heavenly Ambassadors ne ya faɗa mata cewa ubangiji ya nuna masa cewa arzikin ta na ƙasar waje.

Safarar mutane ya zama ruwan dare a ƙasashen duniya da dama musamman ƙasashe masu tasowa.

Rahoton UNESCO ne 2016 ya ruwaito cewa talauci ne babban dalilin da yasa mata da yara suke faɗa wa hannun masu safarar mutane kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

Kafin ta tafi Rasha, Ehioze ya sada Florence da mahaifiyarsa Vivian Ehioze aka kai ta inda ta yi rantsuwa cewa ba za ta gudu ba idan ta isa Rasha.

Daga bisani an faɗa mata ta biya $46,000 ta ƴanci kanta daga karuwancin idan kuma ta yi yunƙurin tserewa za a kashe ta.

Florence ta bayyana cewa ta sha baƙar wahala a Rasha inda wasu mazan suke kwanciya da ita su ƙi biya wasu lokutan har da su mata barazanar kisa.

KU KARANTA Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi

"Rayuwa ta kullum cikin hatsari ta ke. Wasu lokutan zan yi mako guda ba hutu ina harka da maza. Wasu suna da bindiga. Wasu lokutan tsirara na ke tsere wa da tsakar rana kada su kashe ni," in ji ta.

Matar da aka damƙa ni hannun ta kuma ba ta damu da halin da na ke ciki ba ita dai kullum ta ga kuɗi kawai.

"Akwai lokacin da na tafi kwana da wani aka turo ni daga bene na 3 na karya hannu, na yi wata biyu a gida ina jinya, matar da ke kula da ni har cewa ta yi in fita a hakan in cigaba da neman kuɗi," ta ce.

Daga bisani an dawo da Florence Najeriya bayan ta yi fama da wani ciwo da aka rasa gano kansa.

Tun bayan dawowar ta Najeriya a 2017, ta mayar da hankali wurin aikin ta a matsayin mai gyaran gashi.

Daga baya dai hukuma sun kama faston da mahaifiyarsa a jihar Edo saboda rawar da suka taka wurin safarar Florence.

An gurfanar da su a babban kotun jihar Edo kan tuhumarsu da laifin safarar mutane.

A wani labarin daban, Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane na Ƙasa, NAPTIP ta ce ta ceto mutane 135 tare da kama mutum 86 da ake zargin masu safarar mutane ne a Kano daga watan Janairu zuwa yanzu.

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Shehu Umar ne ya bayyana hakan yayin hirar da Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta yi da shi ranar Talata a Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel