Mayaƙan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, mutane 8 sun mutu

Mayaƙan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, mutane 8 sun mutu

- Yan ta’addan Boko Haram sun sake kai hari Borno, sun kashe mutum takwas

- Daya daga cikin wadanda suka tsere daga kauyen ya yi ikirarin cewa an kashe mutum takwas yayinda biyu suka raunana

- Harin ya afku ne yan kwanaki bayan kakakin majalisar dokokin jihar ya ce kananan hukumomi uku sun zama wayam saboda ta’addanci

Yan ta’addan Boko Haram sun sake kai mummunan hari jihar Borno a daren ranar Talata, 15 ga watan Satumba.

Jaridar Sun ta ruwaito cewa harin wanda ya afku a kauyen Wasaram ya yi sanadiyar mutuwar mutum takwas yayinda wasu biyu suka jikkata.

Ali Musa, daya daga cikin mutanen da suka tsere daga kauyen zuwa jihar da ke makwabtaka ta Yobe ya ce yan ta’addan sun kai kimanin su 30.

KU KARANTA KUMA: Duk da bakar wahalar dana sha a kasar Libya, har yanzu ina son komawa can

Mayaƙan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, mutane 8 sun mutu
Mayaƙan Boko Haram sun kai sabon hari a Borno, mutane 8 sun mutu Hoto: The Guardian
Asali: UGC

“Sun zo Wasaram da misalin karfe 8:00 na dare a ababen hawa. Sun kai kimanin su 30. Sai suka fara harbin mutane daga mashigin kauye. Mutane takwas aka kashe sannan aka raunana biyu a harin,” Musa ya bayyana.

Da farko, Legit.ng ta ruwaito cewa kakakin majalisar dokokin jihar Borno, Abdulkareem Lawan, a ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba, ya ce akalla kananan hukumomi uku na jihar sun zama fayau sakamakon hare-haren yan ta’adda.

Kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da - Guzamala, Marte da Abadam, duk a yankin arewacin jihar.

KU KARANTA KUMA: Kano: Mutane uku sun mutu sakamakon rushewar wani a gini a Dawanau

Kakakin majalisar ya bayyana hakan ne bayan rahotanni sun billo cewa sojoi tara da wasu mayakan ISWAP sun rasa ransu a wasu musayar wuta mabanbanta da suka yi a kananan hukumomin Magumeri da Kukawa a ranar Talata, 1 ga watan Satumba.

A wani labarin, Obadiah Mailafia, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, ya ce bai da hujjar da zai marawa ikirarinsa kan masu daukar nauyin Boko Haram baya.

Hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta gayyaci Mailafia a watan Agusta kan ikirarinsa na cewa wani gwamnan arewa ne shugaban Boko Haram.

Bayan DSS ta sake shi, Mailafia ya ce ya shirya sadaukar da rayuwarsa ga kasar kamar yadda Nelson Mandela, tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, yayi wa kasarsa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel