Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya - Shugaba Buhari

Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya - Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya bayyana cewa Najeriya kasar bakar fata da tafi kowacce kasa cigaba a duniya

- Haka a bangaren tattalin arziki, shugaban kasar ya bayyana cewa Najeriya ce kan gaba a Afrika

- Shugaban kasar ya bayyana hakane a wajen taron cika Najeriya shekaru 60 da samun hadin kai a Abuja

A yayin da Najeriya ke shirin bikin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Najeriya a matsayin kasar bakar fata da suka fi kowa samun cigaba a duniya da kuma tattalin arziki.

Shugaban kasar ya bayyana hakane a yau 16 ga watan Satumba a babban birnin tarayya Abuja.

Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya - Shugaba Buhari
Najeriya ce kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya - Shugaba Buhari
Source: Twitter

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar Femi Adesina, ya fitar, shugaban kasar yana cewa:

"A yau mun zaya akan abubuwa na tarihi, inda muka fara gabatar da bukukuwa na murnar cikar Najeriya.

"Murnar cika shekaru 60 da samun 'yancin kai na da muhimmanci, amma cutar COVID-19, wacce ta addabi kowacce kasa ta duniya ta sanya komai ya canja, hakan ya sanya muka gabatar da bikin ba kamar yadda aka saba gabatarwa ba.

KU KARANTA: Duk da bakar wahalar dana sha a kasar Libya, har yanzu ina son komawa can

"Najeriya kasa dake da yawan mutane sama da miliyan 200, da suke da tsantsar basira, muna da matukar muhimmanci a idon duniya. Waannan a gare ni wani abun alfahari ne. Duk inda ka shiga a duniya, 'yan Najeriya ne kan gaba, ko a bangaren ilimi, bangaren kasuwanci, bangaren cigaba, bangaren nishadi, bangaren al'ada da sauransu.

"Haka kuma hoton gwal dake jikin taswirar mu ta nuna cewa muna da matukar muhimmanci, 'yan Najeriya na da matukar muhimmanci a idon duniya. Duka wadannan abubuwa sune suka saka muka zama kasar da tafi kowacce kasar bakar fata cigaba a duniya, sannan kuma ta zama kasar da tafi kowacce karfin tattalin arziki a Afrika. Wannan babban abin alfahari ne ga mutanen da suke aiki sau da kafa domin cigaban kasar."

KU KARANTA: Ka kyale Obaseki, ka fuskanci makiyan siyasa na APC - PDP ga Tinubu

Shi kuwa tsohon ministan jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya ce har sai shugaban kasa Muhammadu Buhari ya canja takunsa akan tafiyar da lamarun Najeriya, sannan komai zai dawo daidai, idan ba haka ba kuma nan da 2023 za a nemi Najeriya a rasa.

Femi Fani Kayode ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya da daddare.

Wannan rubutu na shi dai ya zo ne kwanaki kadan bayan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa Najeriya na cigaba da lalacewa a hankali a hankali a karkashin gwamnatin shugaba Buhari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel