Jihar Binuwai ta yi umurnin bude makarantu a ranar 21 ga watan Satumba

Jihar Binuwai ta yi umurnin bude makarantu a ranar 21 ga watan Satumba

- Gwamnatin jihar Binuwai ta sanar da batun bude dukkanin makarantu a fadin jihar

- Farfesa Dennis Ityavyar, kwamishinan ilimi na jihar ne ya sanar da hakan

- Gwamnatin ta saka ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, a matsayin ranar komawar dukkanin makarantu na gwamnati da na kudi

Gwamnatin jihar Binuwai ta amince da komawa makarantu a fadin jihar a ranar 21 ga watan Satumba, 2020.

Kwamishinan ilimi na jihar, Farfesa Dennis Ityavyar ya sanar da hakan a ranar Laraba, a gidan gwamnati da ke Makurdi yayinda yake zantawa da manema labarai.

Ya bukaci makarantun kudi da na gwamnati kama daga firamare, sakandare da jami’a duk su bi umurnin.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi

Ya kuma yi bayanin cewa za a koma zango na farko ne, inda yace an soke zango na uku da biyan kudin zango na uku illa ga daliban JSS 3 da SSS 3.

Jihar Binuwai ta yi umurnin bude makarantu a ranar 21 ga watan Satumba
Jihar Binuwai ta yi umurnin bude makarantu a ranar 21 ga watan Satumba Hoto: benuestategovt
Asali: Twitter

“Bari na yi magana sosai kan batun kudin makaranta saboda idan an soke zango na uku, toh an soke kudin zango na uku ma. Amma ta bangaren yan JSS 3 da SSS 3, iyaye za su biya kudinsu na zango na uku, hakan take ga makarantun kudi da na gwamnati,” in ji Farfesa Ityavyar.

A cewar kwamishinan ilimin, hukuncin ya fito ne daga masu ruwa da tsaki a fannin ilimi na jihar, cewa a yiwa dukkanin makarantun gaba da sakandare feshi sannan a bi ka’idojin COVID-19 sosai.

Ya bayyana cewa iyaye za su samar da takunkumin fuska da abun kashe kwayoyin cuta na hannu yayinda hukumomin makarantu za su samar da wajen wanke hannu da kuma kula da tsarin barin tazara a tsakani wajen zama.

Farfesa Ityavyar ya bayyana cewa makarantu dake da yawan dalibai za su yi aiki da safe da kuma rana domin guje na cunkoso, inda yace za a zuba idanu sosai kan haka.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sanar da dalilin hana shigo da kayan abinci kasar nan

Kwamishinan wanda ya yaba da yadda mutane ke bin dokar COVID-19, ya ce zango na farko zai kare a ranar 18 ga Disamba 2020.

Hakazalika za a dawo zango na biyu a ranar 7 ga watan Janairun 2021, sannan ya zo karshe a watan Maris.

A wani labarin, Majalisar dinkin Duniya ta bukaci gwamnatin Najeriya ta kare yaran makaranta da malamai daga hare-haren miyagu yayin da ake maganar sake bude makarantu.

A lokacin da ake tunanin yadda za a dawo karantar da yara a Najeriya, wani babban jami’in UN, Edward Kallon, ya yi kira ga gwamnati ta tabbatar za ta kare jama’a.

Edward Kallon ya yi wannan kira ne a ranar Talata, 8 ga watan Satumba, 2020 domin tuna ranar kare ilmi ta Duniya wanda aka soma gudanarwa a shekarar bana.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel