Wata sabuwa: Lauyar Magu ta gano wani dakin sirri a fadar shugaban kasa

Wata sabuwa: Lauyar Magu ta gano wani dakin sirri a fadar shugaban kasa

- Zainab Abiola ta bayyana cewa akwai dakin ajiye masu laifi a Aso Rock, fadar shugaban kasar Najeriya

- Lauyar ta bayyana hakan bayan an kama wata a gabanta

- Abiola ta kasance lauyar Ibrahim Magu, dakataccen shugaban EFCC

A wani lamari da zai zo wa yan Najeriya da dama da ban al’abi, lauyar Ibrahim Magu, dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), ta bayyana cewa akwai dakin ajiye masu laifi a Aso Rock.

Ta bayyana hakan ne yayinda take zantawa da jaridar The Cable game da yadda aka kore ta daga gaban kwamitin da ke bincike cikin zargin rashawa da ake yiwa wanda take karewa.

Lamarin ya afku ne lokacin da kwamitin da Ayo Salami ke jagoranta, yaki barin Abiola da Aliyu Lemu su hade da Wahab Shittu, jagoran lauyoyin Magu, a dakin binciken.

KU KARANTA KUMA: Zargin majalisar tarayya kan badaƙalar NDDC - Akpabio ya yi amai ya lashe

Wata sabuwa: Lauyar Magu ta gano wani dakin sirri a fadar shugaban kasa
Fadar shugaban kasa Hoto: The Cable
Asali: UGC

A cewarta, ba daidai bane kwamitin ya hana lauyoyin Magu shiga zaman.

“Wannan tauye damokradiyya ne, ba zai yiwu ku kawo tsarin mulkin sojoji ba,” in ji ta.

“An kafa wannan kwamiti ne domin yayi aiki a bayyane. Ta yaya ya zamo zama na sirri tare da sarki salam? Ya zama sarki. Ya fada mun da kansa cewa kujera daya ne kawai na lauya. Don haka sai nace, idan kujera daya ne na lauya ka aika a karo kujeru.

“Sai ya kira jami’an DSS, sun kasance dauke da makamai. Don haka sai muka fita. Amma sai aka kama dayar matar, Fatimah, sannan aka jefa ta dakin ajiye masu laifi, a cikin kurkuku. Toh, dama akwai gidan gyaran halayya a fadar shugaban kasa? Yan Najeriya su tausayawa kansu,” in ji ta.

A baya mun ji cewa an dan samu yamutsi bayan shugaban kwamitin bincike, Ayo Salami, ya umarci wasu lauyoyin Magu su fice daga dakin da da kwamitin ke zamansa a fadar shugaban kasa.

Ayo Salami ne shugaban kwamitin bincike da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kafa domin bankado cin hanci da kwato kadarorin gwamnati.

Salami ya umarci jami'an tsaro su fita da wasu lauyoyin Magu guda biyu; Zainab Abiola da Aliyu Lemu, jim kadan bayan gabatar dasu.

KU KARANTA KUMA: Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi

An fara samun matsala ne bayan Wahab Shitu, shugaban tawagar lauyoyin Magu, ya mike domin gabatar da sauran abokan aikinsa.

Sai dai, Salami ya katsewa Shittu hanzari ta hanyar sanar da shi cewa shine kadai za a bari ya kare Magu. Bayan hakan ne sai ya umarci jami'an tsaro su fitar da sauran lauyoyin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng