Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuka 8, gonaki sun kwashe a Katsina

Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuka 8, gonaki sun kwashe a Katsina

- Hukumar SEMA ta jihar Katsina ta tabbatar da cewa hekta 7,019 na gonaki ambaliyar ruwa ya kwashe

- Sakataren hukumar, Babangida Nasamu, ya ce sama da gidaje 25,961 ibtila'in ya fada wa a fadin jihar

- Ya bada tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta gaggauta kai wa wadanda lamarin ya shafa tallafi domin rage radadi

Hukumar taimakon gaggawa ta jihar Katsina (SEMA), a ranar Talata ta tabbatar da mutuwar rayuka takwas tare da salwantar gine-gine 25,961 da ambaliyar ruwa ta shafa a sassan jihar Katsina.

Babban sakataren SEMA, Babangida Nasamu, ya sanar da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a wata tattaunawa, cewa gonaki hekta 7,019 ruwan saman ya lalata.

Nasamu, wanda ya sanar da hakan ta bakin kakakin hukumar, Umar Mohammed, ya ce kusan mutum 17 ne suka samu miyagun raunika sakamakon annobar da ta fada wa jihar.

Ya sanar da cewa, dukkan kananan hukumomi 34 sai da ibtila'in ambaliyar ya shafesu daga watan Janairun 2020 zuwa yanzu.

Kamar yadda yace, gidaje 103 ambaliyar ruwan ta shafa a karamar hukumar Kankara ta jihar, hakan ne yasa ta zama karamar hukumar da ke da karancin ibtila'in. A cikin karamar hukumar Katsina wacce lamarin ya fi shafa, gidaje 3,568 lamarin ya shafa.

Ya kara da cewa hekta 7,019 ambaliyar ruwan ya shafa kuma amfanin gona na miliyoyin Naira suka lalace a wannan lokacin.

KU KARANTA: FG za ta kwaso 'yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar - Zulum

Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuka 8, gonakin sun kwashe a Katsina
Ambaliyar ruwa ta salwantar da rayuka 8, gonakin sun kwashe a Katsina. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hoto: 'Yan sanda sun cafke matasa 4 a kan dukan dan sanda har ya mutu

Ya ce tuni hukumar ta zagaya inda ta duba yanayin barnar da ta auku, kuma ta tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta tallafawa wadanda abun ya shafa domin rage musu radadi.

Nasamu ya kara da kira ga kwamitin fadar shugaban kasa da ke tallafawa wurin rage radadi da gyara ga wadanda ibtila'in ambaliyar ruwa ya shafa a karkashin ma'aikatar walwala da jin kan 'yan kasa, da ta garzaya domin bai wa jama'a taimako.

A wani labari na daban, a kalla mutum 14 suka rasa rayukansu yayin da gidaje masu tarin yawa suka rushe bayan ambaliyar ruwa da ta auku a karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara a makon da ya gabata.

Jaridar SaharaReporters ta gano cewa, daruruwan mazauna yankin a halin yanzu sun zama 'yan gudun hijira.

Wani mazaunin yankin, ya ce babban mai bada shawara na musamman a kan harkokin tallafi da jin kai na Gwamna Bello Muhammad Matawalle, ya ziyarci yankin kuma ya rarraba kayan abinci ga wadanda lamarin ya shafa.

Ya danganta wannan ibtila'in ambaliyar ruwan da rashin tituna masu kyau a yankin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel