Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi

Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi

- Jam'iyyar PDP reshen jihar Edo ta jinjinawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan zuba matakan tsaro da yawa gabannin zaben gwamnan jihar

- PDP ta ce hakan ya basu karfin gwiwar cewa ba za a samu rikici ba a lokacin zaben, sannan kuma cewa zai ba masu zaben karfin gwiwar fitowa jefa kuri'u

- A ranar Asabar, 19 ga watan Satumba ne dai za a gudanar da zaben gwamna a jihar

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) reshen jihar Edo, ta yi godiya ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan tura isassun tsaro zuwa jihar Edo, gabannin zaben gwamna na ranar 19 ga watan Satumba a jihar, jaridar Leadership ta ruwaito.

Babban sakataren labarai na jam’iyyar a jihar, Chris Osa Nehikhare, ne ya bayyana hakan a yayinda ya zanta da manema labarai a madadin kungiyar kamfen na PDP a Edo.

Ya ce: "kokarin da gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari tayi zuwa yanzu na tabbatar da tsaro da kare mutanen Edo, kafin, lokaci da bayan zabe ya cancanci yabo."

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar APC ta fara shirye-shiryen ladabtar da Ojudu, da wasu mutane 12

Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi
Zaben Edo: PDP ta jinjinawa Buhari kan wani ƙoƙari da ya yi Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Nehikhare ya ci gaba da cewa: “Da wadannan tarin yan sanda, sojoji, jami’an NSCDC da sauran hukumomin tsaro da aka jibge a jihar Edo domin su kula da zaben na ranar Asabar, muna da karfin gwiwar cewa za a yi zabe cikin lumana ba tare da rikici ba.”

Ya kara da cewa: “jajircewar Shugaba Buhari na ba masu zabe a jihar kariya zai ba masu zabe karfin gwiwar fitowa domin su jefa kuri’u."

Kakakin na PDP ya bukaci masu zabe a jihar da su fito kwansu da kwarkwatansu a ranar zabe, domin sake zabar Gwamna Godwin Obaseki ta hanyar jefa kuri’arsu ga jam’iyyar PDP, domin ci gaba da kawo sauyi a fadin hukumomin jihar.

KU KARANTA KUMA: Ondo: Bidiyon yadda zaben gwaji ya haifar da hargitsi yayin da APC ta samu nasara

A wani labarin, babban jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi kira ga al'ummar jihar Edo suyi watsi da gwamna Godwin Obaseki, dake neman zarcewa kan kujerarsa.

A faifan bidiyon da tasahar TVC ta saki, Tinubu ya ce Obaseki ba jarumin demokradiyya bane kuma a yi waje da shi a zaben gwamnan ranar Asabar.

Tinubu na cikin jiga-jigan APC da suka yiwa Obaseki yakin neman zabe a shekarar 2016 karkashin jam'iyyar APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel