A karshe: Buhari ya fadi dalilin gwamnatinsa na yawan ciyo bashi

A karshe: Buhari ya fadi dalilin gwamnatinsa na yawan ciyo bashi

> 'Yan Najeriya suna yawan korafi a kan yawan ranto makudan kudade da gwamnatin shugaba Buhari ke yawan yi

> A karshe shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya kare gwamnatinsa a kan yawan ranto kudade da gwamnatinsa ke yi

> Buhari ya bayyana cewa babbar hikimar gwamnatinsa na ranto kudi shine domin ta yi wasu aiyu da zasu burge ma su sha'awar saka hannun jari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana wasu babban dalilan da ya sa gwamnatinsa take ciyo bashi.

A cewar shugaba Buhari, gwamnatinsa ta na ranto kudade ne domin gudanar da aiyukan raya kasa da zasu jawo hankalin ma su zuba jari a tattalin arziki.

A wani jawabi da kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu, ya fitar, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya yi wannan bayani ne yayin wani taro da mambobin kwamitin bayar da shawara kan tattalin arziki (PEAC).

Shugaba Buhari ya bayyana cewa babbar hikimar gwamnatinsa na ranto kudi shine domin ta yi wasu aiyu da zasu burge ma su sha'awar saka hannun jari, kamar yadda Garba Shehu ya bayyana.

A cewarsa, ya zama dole Najeriya ta gyara hanyoyinta na sufuri domin rage yawan asarar rayuka samakon yawaitar hatsarin motoci.

"Mu na da kalubale mai yawa a bangaren aiyukan raya kasa, akwai bukatar mu karbi rancen kudi domin gina hanyoyi, digar jirgin kasa da lantarki, wadanda sai da su ma su saka hannun jari za su saka kudinsu," a cewar shugaba Buhari bayan ya saurari jawabin shugaban PEAC, Farfesa Ayo Salami.

A karshe: Buhari ya fadi dalilin gwamnatinsa na yawan ciyo bashi
Buhari
Asali: Facebook

Buhari ya nuna takaicinsa a kan yadda Najeriya ta rasa matsayinta na zama cibiyar kasuwanci ta kasashen Afrika ta yamma saboda gwamnatocin baya sun gaza samar da manyan aiyukan da za su gina kasa.

KARANTA: Zaben 2020: Jerin alkawuran da Trump ya cika da wadanda bai cika ba a Amurka

KARANTA: Hotuna: Osinbajo ya wakilci Buhari a taron kungiyar ECOWAS a kasar Ghana

A kan matsin tattalin arziki, Buhari ya alakanta hakan da faduwar darajar man fetur a kasuwar duniya da kuma kayyadewa mambobin OPEC (kungiyar kasashe ma su arzikin man fetur) adadin man da za su fitar.

Buhari ya bayyana cewa rungumar harkar noma ce kadai mafita ga Najeriya, ita ce hanyar da za a rage matsalar zaman kashe wando da kawo karshen talauci.

"Matukar mu na son sauya al'amura dangane da batun kalubalen rashin aiki da yaki da talauci, ya zama wajibi mu koma gona.

"Ba don mun fara komawa gona ba da wahalar da ake ciki sai ta zarce ta yanzu, mun karfafa tare da samar da sabbin dumbin aiyuka ta hanyar dakatar da shigo da abinci," a cewar shugaba Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel