Zaben Edo 2020: Jerin manyan jiga jigan PDP da suka hallara a Benin
- Manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP sun yi wa jihar Edo tsinke a yau Talata, 15 ga watan Satumba
- Sun je Edo ne domin yi wa dan takarar gwamna na jam’iyyar a zabe mai zuwa, Godwin Obaseki kamfen
- Za a dai gudanar da zaben gwamnan na jihar Edo a ranar Asabar, 15 ga watan Satumba mai zuwa
A yanzu haka manyan jiga-jigan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da suka hada da gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike; Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto da Gwamna Seyi Makinde na Oyo suna a Benin.
Sun yi wa babbar birnin na jihar Edo tsinke ne domin yi wa Gwamna Godwin Obaseki, dan takarar jam’iyyar a zaben gwamna mai zuwa kamfen, Channels TV ta ruwaito.
Shugabannin sun hadu ne a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin domin babban gangamin jam’iyyar gabannin zaben gwamnan jihar Edo.
KU KARANTA KUMA: Da zafinsa: Yan bindiga sun kai sabon hari Katsina, sun kashe 1 tare da sace mata
Kakakin jam’iyyar, Kola Ologbondiyan a wajen gangamin ya mika godiya ga tarin jama’a da suka nuna goyon bayansu ga Obaseki.
Sauran shugabanni da suka hallara a taron sun hada da Gwamna Udom Emmanuel na jihar Akwa Ibom; tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha.
Sai kuma Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta; Raymond Dokpesi da sauransu.
Da yake jawabi a wajen taron, tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2019, ya bukaci masu zabe da su fito domin zabar Obaseki a ranar Asabar mai zuwa.
Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Uche Secondus a nasa jawabin ya ce akwai tabbacin Obaseki zai yi nasara duba ga yawan manyan da suka nuna goyon bayansu gare shi.
KU KARANTA KUMA: Bayan karɓar N5m: Yan bindiga sun kashe jami'in DSS a jihar Katsina
A wani labarin kuma, mun ji cewa Gwamna Godwin Obaseki da tsohon gwamnan jihar Kano, Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso, sun kaddamar da sansanin Alhazai a Benin.
Sun kuma bukaci al’umman Musulmi a jihar da su fito kwansu da kwarkwatarsu a ranar 19 ga watan Satumba domin tabbatar da sake zabar Gwamna Obaseki wanda yake dan takarar PDP da mataimakinsa, Rt. Hon. Comr. Philip Shaibu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng