FG za ta kwaso 'yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar - Zulum

FG za ta kwaso 'yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar - Zulum

- Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya tabbatar wa da 'yan gudun hijirar da ke Nijar cewa sun kusa dawowa gida

- Wasu wakilai daga gwamnatin tarayya sun kai wa 'yan gudun hijirar ziyara a yankin Diffa da ke jamhuriyar Nijar

- Sun tabbatar wa da jama'ar Najeriya cewa Shugaba Buhari na yin iyakar kokarinsa domin ganin dawowarsu

Najeriya ta tabbatarwa da 'yan kasar nan da ke gudun hijira a Diffa da ke jamhuriyar Nijar, cewa tana musu shirye-shiryen dawowa gida Najeriya.

Wasu wakilan gwamnatin tarayya da suka zaiyarci kasar, wadanda Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya jagoranta, sun sanar da masu gudun hijirar cewa sun je duba halin da suke ciki domin ganin yadda za a kwashesu tare da dawo da su gida Najeriya.

Kamar yadda takardar da ta fito daga hannun Nneka Ikem, mai bai wa ministan tallafi da jin kai shawara, Sadiya Umar Farouk, ta bayyana, gwamnatin tarayyar na iyakar kokarin da ya dace.

Ministar walwala da jin kan 'yan kasa, Sadiya Umar Farouk ta samu rakiyar shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira, Sanata Basheer Garba Mohammed.

Kamar yadda takardar ta bayyana, shugaban hukumar ya samu wakilcin babban daraktan ofishin babban sakatensa, Alhaji Ali Grema, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: La-liga: Ali Nuhu ya zama Jakadan kwallon kafa a Arewacin Najeriya

FG za ta kwaso 'yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar - Zulum
FG za ta kwaso 'yan Najeriya da ke gudun hijira a Nijar - Zulum. Hoto daga Vanguard
Source: Twitter

KU KARANTA: Baka damu da mawuyacin halin da 'yan Najeriya ke ciki ba - Kungiyoyi a Kano sun caccaki Buhari

"A yayin ziyarar, Gwamna Zulum ya tabbatar wa da 'yan gudun hijirar da ke kasar Nijar cewa, shugaban kasa Muhammdu Buhari ya mayar da hankali wurin ganin sun dawo gida lafiya kuma suun koma cikin 'yan uwansu.

"Wakilan sun samu ganawa da Gwamna Isa Lameen na yankin Diffa tare da zagayawa domin ganin yadda ake gina wasu gidajen wucin-gadi har guda 1,000 a garin Damasak da ke kusa da iyakar Najeriya," takardar tace.

A wani labari na daban, duk da harin da aka kai wa tawagarsa a garin Baga, Gwamna Babagana Umara Zulum ya cigaba da ayyukan jin kansa a Munguno inda ya kai wa yan sansanin gudun hijira kimanin 80,000 kayan tallafi.

Gwamnan ya isa Munguno a ranar Litinin tare da tawagarsa inda suka raba wa 'yan sansanin gudun hijira kayan tallafi a Marte, Guzamala, Kukawa, Nganzai da Monguna.

An rabar da dubban buhunnan hatsi, man girki da wasu kayayyakin da mutanen da ke sansanin yan gudun hijirar da sauran mabukata a garuruwan da sansanin suke.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel