Ba ni da wata hujja ta cewar gwamnonin Arewa ne ke ɗaukar nauyin Boko Haram - Mailafia

Ba ni da wata hujja ta cewar gwamnonin Arewa ne ke ɗaukar nauyin Boko Haram - Mailafia

- Obadiah Mailafia ya ƙaryata kansa kan zargin gwamnonin Arewa da daukar nauyin Boko Haram

- Mailafia ya ce bai da kwakkwaran hujja a kan haka cewa shima ji yayi a wajen wasu yan kasuwa

- Sai dai yace da ace yana da dama toh da ya gyara wasu daga cikin kalamansa na baya

Obadiah Mailafia, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya ce bai da hujjar da zai marawa ikirarinsa kan masu daukar nauyin Boko Haram baya.

Hukumar tsaro na farin kaya (DSS) ta gayyaci Mailafia a watan Agusta kan ikirarinsa na cewa wani gwamnan arewa ne shugaban Boko Haram.

Bayan DSS ta sake shi, Mailafia ya ce ya shirya sadaukar da rayuwarsa ga kasar kamar yadda Nelson Mandela, tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, yayi wa kasarsa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya yi sabbin nade-nade masu muhimmanci guda 4

Amma a wata hira da sashin Hausa na BBC, Mailafia ya bayyana cewa ya samu bayanan ne daga wasu yan kasuwa kuma cewa bai san jawabin nasa zai shahara haka ba.

Ba ni da wata hujja ta cewar gwamnonin Arewa ne ke ɗaukar nauyin Boko Haram - Mailafia
Ba ni da wata hujja ta cewar gwamnonin Arewa ne ke ɗaukar nauyin Boko Haram - Mailafia Hoto: Punch
Source: Twitter

Da yake magana a ranar Litinin a garin Jos, babbar birnin jihar Plateau bayan ya amsa tambayoyi karo na uku a hukumar DSS, tsohon Shugaban CBN din yace da ace yana da dama, da ya gyara kalamansa yadda za a fi fahimta.

“Na gurfana a gaban hukumar tsaro na farin kaya, reshen jihar Plateau. Naji dadin yadda aka yi mun cike da kwarewa. Babu cin zarafi ko barazana,” in ji Mailafia.

“Sama da wata guda da nayi hira da wata tashar radiyo, kan abunda naji. Da ace ina da dama toh da na fadi wasu abubuwa ta hanya daban, amma aikin gama ya gama, kuma na yarda cewa akwai bukatar jan hankali na gaggawa game da abunda ke faruwa.

“Ba wai ina nufin cewa gwamnati na da hannu a cikin kashe-kashen da ake yi bane, ina nufin cewa suna iya yin kokari fiye da wanda suke yi saboda dubban mutane na mutuwa, bayin Allah mata da yara, tsoffi da matasa.

“Amma da ace ina da damar gyara kalamaina toh da nayi, kuma bani da hanyar samun bayanai kan wasu daga cikin wadannan abubuwan, na ji ne kuma da na bi su sansanoninsu domin tabbatarwa saboda ba lallai ne na dawo na bayar da labarin ba, wannan shine gaskiyar lamari.

“Na nuna cewa na yarda rayuwata na cikin hatsari. Bani da kwakwaran hujja amma ina samun barazana, ina samun kiraye-kiraye. Inda nake kokarin zama, a ranar Alhamis, na ga wasu bakin mutane a kofar suna kokarin shigowa ciki, na tsallake Katanga sannan na tsere saboda ban san ko su wanene ba.”

KU KARANTA KUMA: Bude boda: Ku ci abinda kuka shuka - Sakon Buhari ga ƴan Nigeria

Magoya bayansa sun taru a kofar ofishin DSS suna ta wake-wake na yabonsa, aridar The Cable ta ruwaito.

A baya mun ji cewa, Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailafia, ya ce rayuwarsa tana cikin garari tare da hatsari.

Mailafia ya sanar da hakan ne a yayin da yake martani a kan gayyatar da jami'an tsaro na farin kaya suka yi masa a karo na uku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel