Obasanjo ya yabawa Buhari, da wasu game da gudumuwarsu wajen sake zaben Adesina

Obasanjo ya yabawa Buhari, da wasu game da gudumuwarsu wajen sake zaben Adesina

- Olusegun Obasanjo ya ce Buhari ya taimakawa Akinwumi Adesina a zaben AfDB

- Obasanjo ya ce Buhari ya nuna dattaku ta yadda ya marawa takarar Adesina baya

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya tofa albarkacin bakinsa a game da zaben bankin cigaban Afrika da aka gudanar ‘yan kwanakin baya.

A ranar Litinin, 14 ga watan Satumba, 2020, Olusegun Obasanjo, ya yabawa kokarin irinsu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari game da zaben.

Tsohon shugaban kasar ya yabi Muhammed Buhari da sauran shugabannin kasashen Afrika a kan goyon bayan da su ka ba Dr. Akinwunmi Adesina a AfDB.

Janar Olusegun Obasanjo mai ritaya ya fitar da wannan jawabi ne ta bakin hadiminsa, Mista Kehinde Akinyemi, a jiya ranar Litinin, 14 ga watan Satumba.

KU KARANTA: Kungiya ta fadawa Buhari da Gwamnoni 36 lakanin kawo zaman lafiya

Wannan jawabi ya fito ne a lokacin da wata kungiya ta ‘yan jarida masu zaman kansu, su ka kai wa tsohon shugaban kasar ziyara a dakin karatunsa da ke Ogun.

Mai girma Olusegun Obasanjo ya gina katafaren dakin karatu a garin Abeokuta, jihar Ogun.

Tsohon shugaban da ya mulki Najeriya har sau biyu, a lokacin mulkin soja da farar hula, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ba Akinwunmi Adesina gudumuwa.

Obasanjo ya ce ilmi ya yi tasiri a wannan zabe da aka yi a AfDB da kuma sauran ‘yan Najeriya da ke rike da manyan mukamai a sauran kungiyoyin da ake ji da su.

Jawabin Obasanjo ya ce: “Dole in yabawa kokarin da gwamnatin tarayya ta yi masa (Dr. Akinwunmi Adesina) na samun tazarce.”

KU KARANTA: Fayose ya ajiye sabaninsa da Obasanjo, ya taya shi yi wa Buhari kaca-kaca

“Kun san cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya mara masa baya kafin wannan gwamnati ta shigo. Da gwamnatin nan ta ga dama, da ta yi fatali da shi.”

Janar Obasanjo ya ce Buhari bai yi hakan ba, sai ya nuna dattako, ya marawa tsohon ministan na Jonathan baya, har ya zama shugaban bankin AfDB.

Obasanjo ya yabawa Buhari, da wasu a kan gudumuwarsu wajen sake zaben Adesina
Dr. Adesina da Shugaban kasa Hoto: Twitter/NgrPresident
Asali: Twitter

A dalilin Obasanjo, tsofaffin shugabannin kasashen Afrika 14 su ka nuna goyon bayansu ga tazarcen Adesina. A karshe ‘dan Najeriyar ya lashe zaben da aka yi.

Tsohon shugaban kasar ya ce akwai wasu shugabanni masu-ci da su ka taka rawar gani.

Idan ba ku manta ba, kwanan nan Obasanjo ya ce abubuwa sun lalace a kasa a karkashin mulkin Buhari, a cewarsa ana samun karuwar talauci da rashin hadin-kai.

Tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, ya na ganin cewa gyaran kasar nan sai Allah domin Obasanjo ya riga ya jikawa gwamnatin Buhari aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel