Boko Haram: Janar Adeosun ne ya ceci rayuwata inji Shugaban Hafsun Soji Buratai

Boko Haram: Janar Adeosun ne ya ceci rayuwata inji Shugaban Hafsun Soji Buratai

- Tukur Yusuf Buratai ya ziyarci Osun, ya kaddamar da wata gadar da aka gina

- Shugaban hafsun sojin kasar ya bada labarin jaruntar Janar Lamidi Adeosun

- Janar Burarai ya ce Mataimakin na sa ya ceci shi a hannun ‘Yan ta’adda a baya

A ranar Litinin, 14 ga watan Satumba, Laftana-Janar Tukur Yusuf Buratai, ya tuno yadda ‘yan ta’addan Boko Haram su ka kai masa hari shekarun baya.

Shugaban hafsun sojin kasa ya tado wannan magana ne wajen kaddamar da wata gada da sojoji su ka gina a garin Kuta, Osun, wanda aka sa wa sunansa.

Jaridar Punch ta ce dakarun sojojin kasa na Ede da su ka kware a harkar fasaha su ka gina gadar.

Tukur Yusuf Buratai ya ce mataimakinsa, Laftana-Janar Lamidi Adeosun shi ne wanda ya ceci rayuwarsa a lokacin da ‘yan ta’adda su ka kai masa hari.

KU KARANTA: Sanata Ndume ya ja-kunnen Gwamnati kan yi Boko Haram afuwa

Janar Burarai da tawagarsa sun fuskanci wani samame a yankin Arewa maso gabashin Najeriya jim kadan bayan an nada shi a matsayin shugaban sojin kasa.

Buratai wanda ya yabawa kokarin dakarun sojojim ya ce lokacin da ya zama shugaban sojoji, ya hadu da Janar Adeosun, wanda ya ce ya fara gyara gidan soja.

Lamidi Adeosun ainihinsa mutumin jihar Osun ne inda shugaban hasfsun sojin ya kai ziyara wajen kaddamar da wannan gada da za ta sa a dade ana tunawa da shi.

A cewar Tukur Yusuf Buratai, an kai masa wannan hari ne yau kusan shekaru biyar da su ka wuce.

KU KARANTA: DSS ta na neman Mahadi Shehu bayan ya jefi Gwamna da zargi

Lamidi Adeosun ya ceci rayuwata inji Shugaban Hafsun Soji Tukur Buratai
Lamidi Adeosun lokacin da ya zama Laftana-Janar Hoto: PMNews
Source: UGC

COAS Tukur Yusuf Buratai ya ce: “Lokacin da aka kai mani samamen farko, (Adeosun) ya na tare da ni a cikin mota. A ranar 18 ga watan Satumban 2015 ne.”

Ya ce: “Kuma na ga irin jaruntar da ya nuna.”

“Ya yi kokarin tattaro dakaru su maidawa ‘yan ta’addan martani, su ka sa ‘yan bindigan su ka bar wurin. Saboda haka karin matsayin da aka yi masa bai ba ni mamaki ba.”

“Ya cancanci karin matsayin da aka yi masa.”

Kwanakin baya Lamidi Adeosun ya samu karin matsayi inda ya zama Laftana-Janar, daga shi sai mai gidansa, Tukur Yusuf Buratai kadai su ke da wannan girma a sojojin kasar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel