TUC, NECA, da ASUU, sun yi Allah-wadai da karin farashin lantarki da fetur

TUC, NECA, da ASUU, sun yi Allah-wadai da karin farashin lantarki da fetur

- TUC ta ba Gwamnati wa’adin mako guda ta janye karin da ta yi na mai da wuta

- Kungiyar ta ce idan ba ayi haka ba, za ta tafi yajin aiki daga 23 ga Satumban nan

- Gwamnatin Tarayya ta na sa ran shawo kan TUC da sauran kungiyoyin ma’aikata

A jiya ne kungiyar TUC ta ‘yan kasuwan Najeriya, ta bayyana cewa za ta tafi yajin aiki muddin gwamnatin tarayya ba ta janye karin kudin mai da wutar lantarki ba.

TUC ta bukaci shugaba Muhammadu Buhari ya yi maza ya dakatar da karin da ya yi, ko kuma ya gamu da mummunan yajin aiki a fadin kasar nan na kwanaki bakwai.

A wata takarda da kungiyar ta fitar a ranar 14 ga watan Satumba ta bakin shugabanta da kuma sakatarensa, Quadri Olaleye da Musa Lawal, sun soki karin da aka yi.

KU KARANTA: Karin kudin wuta ya jawo zanga-zanga a Najeriya

A cewar ‘yan kasuwar, mutanen Najeriya ba za su iya cigaba da jure manufofin da gwamnatin tarayya ta ke kawowa, TUC ta ce manufofin ba su so talaka ya numfasa.

Kungiyar TUC ta fitar da matsayarta ne a lokacin da ta gabatar da wasikarta gaban ‘yan jarida jiya.

Ita kuma kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta yi Allah-wadai da yadda gwamnatin tarayya ta saida Najeriya ga burin kungiyar lamuni ta IMF da babban bankin Duniya.

Shugaban ASUU, Farfesa Biodun Ogunyemi, a wata hira da ya yi da jaridar Punch a Legas, ya ce gwamnati ta shiryawa ganin fushin al’umma a dalilin karin kudin da aka yi.

KU KARANTA: Malami ya soki karin da aka yi a kan kudin wuta

TUC, NECA, da ASUU, sun yi Allah-wadai da karin farashin lantarki da fetur
Gidan mai a Najeriya Hoto: Facebook
Asali: UGC

A cewar malaman jami’ar, masu rike da madafan iko a Najeriya, ba su kaunar mutanen kasa.

Ogunyemi ya ja-kunnen gwamnatin APC mai-mulki a kan yawan dogaro da biyewa kungiyoyin kasar waje irinsu IMF mai bada lamuni a Duniya da kuma babban banki.

Idan ba za ku manta ba, a farkon watan nan ne aka kara farashin sarin man fetur daga N138.62 zuwa N147.67, hakan ya jawo aka koma sayen mai a gidajen mai a N160.

Bayan haka, an kara kudin shan wutar lantarki a daidai lokacin da jama’a su ke wayyo. Gwamnati ta na sa rai a zaman da za ta yi a makon nan, ta shawo kan kungiyoyi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel