Magudin zabe: Amurka haramta wa wasu manyan 'yan Najeriya shiga kasar ta

Magudin zabe: Amurka haramta wa wasu manyan 'yan Najeriya shiga kasar ta

- Amurka ta saka wa wasu ƴan Najeriya takunkumin shiga kasar ta saboda munannan rawar da suka taka yayin zaben gwamna da aka yi a wasu jihohin Najeriya

- Sanarwar da ta fito daga Sakataren Gwamnatin Amurka, Mike Pompeo ta ce an dauki wannan matakin ne don ƙarfafa demokradiyya a Najeriya

- Wadanda aka haramta wa shiga Amurka sun da hannu ne wurin tafka magudin zabe a jihohin Kogi da Bayelsa

Gwamnatin Amurka ta ce ta saka wa wasu mutane takunkumi hana su shigar ƙasar ta saboda magudin zabe da suka yi yayin zabukkan gwamna a jihohin Kogi da Bayelsa da aka yi a 2019.

Wannan na zuwa ne a lokacin da ake shirin yin zabukkan gwamnoni a jihohin Edo da Ondo a watan Satumba da Oktoba na 2020.

Magudin zabe: Amurka haramta wa wasu manyan 'yan Najeriya shiga kasar ta

Magudin zabe: Amurka haramta wa wasu manyan 'yan Najeriya shiga kasar ta. Hoto daga The Punch
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gana ya san zai mutu, ya nada wanda zai gaje shi

Duk da cewa ba riga an yi zabuka a Edo da Ondo ba, Sakataren Gwamnatin Amurka Mike Pompeo ya ce akwai wasu da aka haramta musu shiga kasar ta Amurka.

Hakan ne cikin wata sanarwa ne mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun ma'aikatar wajen Amurka, Morgan Ortagus da ya fitar a ranar Litinin.

"A watan Yulin 2019, mun sanar da haramta wa wasu ƴan Najeriya da suka yi magudin zabe a zabukkan Fabrairu da Maris na 2019 shiga kasar mu.

"A yau, Sakataren Gwamnati ya ƙara saka takunkumin a kan wasu mutane saboda abubuwan da suka aikata da ke da alaƙa da zaɓukkan da aka yi a Nuwamban 2019 a jihohin Kogi da Bayelsa da kuma zabukkan da ke tafe a watannin Satumba da Oktoban 2020 a jihohin Edo da Ondo.

KU KARANTA: An sace motar da aka bawa bakanike gyara yayin da ya tafi gidan karuwai da motar

"Wadannan mutane sun aikata munannan ayyuka da suka shafi ƴan Najeriya kuma sun ruguje wasu shika-shikan demokradiyya," a cewar wani sashi na sanarwar.

Duk da cewa Amurka ba ta ambaci sunayen mutanen da ta saka wa takunkumin shigar ƙasar tan ba, ta ce ta yi hakan ne a matsayin matakin na ƙarfafa demokradiyya a Najeriya.

A wani labarin daban, kun ji cewa Garba Shehu, Kakakin Shugaba Muhammadu Buhari ya ce farashin kayayyakin abinci suna sauka a kasuwanni akasin ƙorafin da mafi yawancin mutanen ke yi.

Garba ya yi wannan furucin ne yayin hirar da aka yi da shi a ranar Juma'a 11 ga watan Satumba a Channels TV da ya ke magana a kan umurnin da Buhari ya bawa bankin ƙasa CBN na dena yiwa masu shigo da abinci da kayan noma canjin kuɗi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel