NAFDAC ta ce Gwamnati za ta rage karfin giyar da ake yi a cikin leda da ‘yan robobi

NAFDAC ta ce Gwamnati za ta rage karfin giyar da ake yi a cikin leda da ‘yan robobi

- Gwamnatin Tarayya za ta rage karfin giyan da ake yi a cikin ledoji

- NAFDAC ta ce giyan da ke zuwa a yan ledoji da robobi su na da karfi

- Hukuma za ta yi kokarin ganin kason ruwan giya bai zarce 30% ba

A karshen makon da ya gabata ne gwamnatin tarayya ta sanar da matakin janye giyan da ake yi a cikin leda da kuma robobi daga kasuwannin Najeriya.

Hukumar NAFDAC ta bayyana shirinta na ganin mutane sun rabu da shan giyar leda da wadanda su ke zuwa a gorar polyethylene terephthalate, watau PET.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin shugabar hukumar NAFDAC mai kula da kwayoyi da abinci, Mojisola Adeyeye. Jaridar The Cable ta bayyana haka.

KU KARANTA: Giya ta kashe 'Dan shekara 48 bayan ya lashe gasar maye

Farfesa Mojisola Adeyeye ta fitar da jawabin ta na cewa rashin kaidi da yawan irin wadannan sirkakkun giya a kasuwa ya na jawo yawan maye a Najeriya.

A cewar, Adeyeye, NAFDAC ba za ta cigaba da yi wa giyan da ake yi a cikin leda ko kuma kananan robobi na PET rajista ba saboda mayen da su ke jawowa.

NAFDAC ta ce Gwamnati za ta rage karfin giyar da ake yi a cikin leda da ‘yan robobi

Mojisola Adeyeye Hoto: This Day
Source: UGC

Da zarar an samu akalla kashi 30% na giya a cikin wadannan ruwa da ke zuwa a leda ko kuma gorar roba, gwamnatin tarayya ba za ta yi masu rajistar NAFDAC ba.

Shugabar NAFDAC ta kasa, Mojisola Adeyeye, ta ce sun zauna da ma’aikatar lafiya, da duk sauran masu ruwa-da-tsaki a wannan harka, kuma sun cin ma matsaya.

KU KARANTA: Yadda ya mutu yayin da mu ke tarawa - Mai zaman kanta

“Game da giya, mun zauna da manyan masu harkar, an wayar da kansu a kan lamarin. A nan, an ci ma yarjejeniya tsakanin masu ta-cewa, kuma ana dabbaka matakan.”

“Bayan haka, domin rage yawa da kuma buguwar da aka saba daga 31 ga watan Junairu, 2020, masu hada giya a ‘yan ledoji da kananan robobin PET da kwalabe za su rage 50% na giyar da su ke yi.”

Farfesa Adeyeye ta cigaba da cewa: “Burin shi ne a rage karfin giyan da ake samu a ledoji da kananan robobi kamar yadda aka tsara a baya.”

Kwanakin baya kun ji cewa rahoton da aka fitar ya nuna duk Afrika babu kasar da ake shan giya kamar Najeriya. Adadin ‘yan giya a kasar ya na ta karuwa tun daga 2015.

A Najeriya, akwai kamfanonin yin giya guda takwas. Mafi yawan wadannan kamfanoni su na zaune ne a yankin Kudancin kasar, idan babu dokar da ta ke fada da barasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Online view pixel