Edo 2020: Yadda wanda na gada ya dinga rantowa jihar kudi yana watanda da su - Obaseki

Edo 2020: Yadda wanda na gada ya dinga rantowa jihar kudi yana watanda da su - Obaseki

- Godwin obaseki, gwamnan jihar Edo ya sanar da yadda gwamnatin da ta gabata a jihar ta dinga cin bashi

- Ya sanar da hakan yayin da yake amsa wasu tambayoyi da aka masa a ranar Lahadi a muhawarar da yayi da abokin adawarsa

- Duk da yawan basussukan, Obaseki ya jinjinawa gwamnatinsa ta yadda yake biyan bashin tare da ayyukan ci gaba ga 'yan jihar

Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya zargi wanda ya gada, Adams Oshiomhole, da saka jihar ciki matsanancin bashi sakamakon yadda ya dinga ciwo bashi babu tsagaitawa.

Obaseki ya sanar da wannan zargin a ranar Lahadi yayin da ake muhawara da shi na zaben gwamnan jihar Edo da ke gabatowa a gidan talabijin na Channels.

"Bari in yi muku wani bayani, abinda ya faru shine yadda wanda na gada ya dinga cin bashi kuma gwamnatin tarayya ce ta sake gayara bashin da aka ci kafin in hau kujerar gwamna," Obaseki ya sanar yayin amsa tambayoyi a kan yawan bashin da ake bin jihar.

"Wannan ya hada da basussukan banki. Gwamnatin tarayya ce ta sake gyara bashin da ake bin jihar Edo har naira biliyan talatin. Wannan ne ya sake kara yawan bashin da ake bin jihar," yace.

KU KARANTA: Yan sanda sun kama wani da yayi fim din batsa da kayan mabiya wani addinin gargajiya a Ogun

Edo 2020: Yadda wanda na gada ya dinga rantowa jihar kudi yana watanda da su - Obaseki

Edo 2020: Yadda wanda na gada ya dinga rantowa jihar kudi yana watanda da su - Obaseki. Hoto daga Channels TV
Source: Twitter

KU KARANTA: 'Yan sanda sun cafke makusancin Gwamna Yari yana taron sirri da 'yan bindiga a Zamfara

Ya kara da zargar gwamnatin da ta gabata da rike kudin kwangiloli da za su kai na biliyan saba'in. Hakan yasa yawan bashin jihar ya kai biliyan 120.

Duk da yawan basussukan, Obaseki ya jinjinawa mulkinsa a kan yadda suke rage yawan bashi da kuma yadda yake samar da cigaban da ya dace ga jama'a.

A wani labari na daban, jam'iyyar All Progressives Congress, APC a jihar Edo ta samu koma baya a ƴunkurin ta na karbe mulki daga hannun jam'iyyar PDP a jihar Edo.

Wannan na zuwa ne bayan mambobin APC fiye da 5,000 sun fice daga jam'iyyar sun koma PDP. Sun kuma jaddada goyon bayansu ga tazarcen Gwamna Godwin Obaseki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel