Ya kamata ka sani, ƴan Nigeria na shan bakar wahala - Jega ya aikawa Buhari sako

Ya kamata ka sani, ƴan Nigeria na shan bakar wahala - Jega ya aikawa Buhari sako

- Attahiru Jega, tsohon shugaban INEC da John Onaiyekan, jigon Katolika sun koka kan halin da yan Najeriya ke ciki

- Sun bukaci shugaba kasar Muhammadu Buhari ya dauki matakin da ya dace

- Jega ya ce yan Najeriya na fama da wahala biyu na rashin tsaro da annobar korona

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Attahiru Jega; da tsohon shugaban malaman Katolika a Abuja, Cardiac John Onaiyekan, sun yi martani kan halin da jama’a ke ciki.

Sun fada ma shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa yan Najeriya na fuskantar wahala biyu na rashin tsaro da kuma na annobar coronavirus.

Don haka sun yi kira ga Shugaban kasar da ya yi duk abunda zai iya domin magance matsalar tsaro koda hakan na nufin sallamar shugabannin tsaro.

Sun bayyana hakan a cikin wani jawabi mai taken, ‘Ya shugaban kasa, Gwamnoni: Yanzu ne lokacin tattaunawa’ a ranar Lahadi.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya tarar da barna a kasa, amma ya kara tabarbarar da abubuwa, in ji Balarabe Musa

Jawabin na dauke da sa hannun Jega, Onaiyekan, Janar Martin Agwai, Amb. Fatima Balla, Farfesa Jibrin Ibrahim, Misis Aisha Muhammed-Oyebode, Dr. Nguyan Feese.

Sai Dr. Usman Bugaje da Dr. Chris Kwanja, dukkaninsu mambobin kungiyar Najeriya kan zaman lafiya da shugabanci nagari ne.

Ya kamata ka sani, ƴan Nigeria na shan bakar wahala - Jega ya aikawa Buhari sako

Ya kamata ka sani, ƴan Nigeria na shan bakar wahala - Jega ya aikawa Buhari sako Hoto: Fadar shugaban kasa
Source: Facebook

Jawabin ya zo kamar haka: “Najeriya, kamar dukkanin kasashen duniya tana fama da annobar korona. Sai dai, al’umman Najeriya na fuskantar wahala biyu ne saboda suna kuma fama da rashin tsaro da rikici a fadin kasar.

“Ya zama dole gwamnatin Najeriya ta dauki matakin gaggawa wajen magance hauhawan rashin tsaro, idan tana son cimma nasara a yaki da annobar. Wani binciken USIP na bayan nan a Najeriya ya gano sabon alaka tsakanin COVID-19, rashin zaman lafiya da kuma rikici.

“Musamman, binciken ya gano cewa wadanda rikice-rikice ya cika dasu ba za su aminta da matakan gwamnati na yaki da annobar korona ba idan aka kwatanta su da wadanda rikicin bai shafa ba.

Sun kuma bayar da shawarwari kan yadda gwamnatin Najeriya za ta iya karfafa kokarinta na daidaita annobar ta hanyar magance rashin tsaro a fadin kasar.

“Garkuwa da mutane don kudin fansa ya kasance babban abun damuwa a fadin kasar. Yankin arewa maso gabas na fuskantar fawowar ayyukan Boko Haram, sannan yan bindiga sun mayar da dubban mutane marasa galihu a fadin garuruwan karkara a arewa maso yamma.

“Miyagun ayyuka a yankunan karkara na kara tabarbarar da lamarin tsaron abinci, domin manoma da dama basa iya zuwa gonakinsu tsawon watanni da dama saboda tsoron rasa ransu,” in ji kungiyar.

Sun yi kira ga Shugaban kasar a kan ya shirya wani tsari na tattaunawa domin magance rikici da ake samu na kabilanci da na addini.

Kungiyar ta ce majalisar kasa a jiha ya jagoranci shirin tattaunawar a matakin kasa yayinda kungiyar gwamnonin Najeriya za ta tabbatar da lamarin ya isa ga talakawa.

KU KARANTA KUMA: Jerin jihohi 28 da za su fuskanci ruwan sama mai tsanani kafin karshen 2020

Sun bayyana cewa rikici tsakanin makiyaya da manoma ya yi sanadiyar rasa dubban rayuka a kasar sannan yana kara zurfafa rikicin kabilanci amma yan tsirarun mutane aka hukunta kan haka.

Don haka kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta yi umurnin sake bincike a kan dukkanin rikicin makiyaya da manoma na baya.

Sun bukaci gwamnati da ta sallami shugabannin tsaro idab hakan ne zai kawo ci gaban abubuwa.

A wani labari na daban, tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, ya ce tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayar da gudunmawa wajen saka Najeriya a halin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya risketa na tabarbarewa.

Jigon kasar na martani ne ga furucin da Obasanjo ya yi a kwanan nan game da gwamnatin Buhari.

Tsohon shugaban Najeriyan ya caccaki Shugaba Muhammadu Buhari, kan yanda yake tafiyar da harkokin kasar, inda ya yi gargadin cewa Najeriya na lalacewa cikin sauri a karkashin mulkin Shugaba Buhari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel