Yi wa ‘Yan ta’adda afuwa yanzu ba zai kawo zaman lafiya ba inji Sanata Ndume
- Sanata Ali Muhammad Ndume ya yi magana game da rikicin Boko Haram
- Ndume ya ce bai dace a rika yi wa Boko Haram afuwa ana cikin yaki ba
- ‘Dan Majalisar ya ce gwamnati ba ta kama hanyar kawo zaman lafiya ba
Shugaban kwamitin sojojin kasa a majalisar dattawa, Ali Muhammad Ndume ya yi gargadi cewa yi wa tubabbun ‘yan ta’adda ba zai kai ga ci a Najeriya ba.
Sanata Ali Muhammad Ndume ya na da ra’ayin cewa yi wa ‘yan ta’adda afuwa, ba zai kawo zaman lafiya a jihohin da ake fama da matsalar rashin tsaro ba.
‘Dan majalisar dattawwan ya ke cewa an kammala duk wasu shirye-shirye na dauke mutane daga sansanin gudun hijira a watan gobe, zuwa ainihin kauyukansu.
A cewarsa mutanen Damboa, Kukawa, Kawuri da yankin Ngoshe sun kusa komawa gidajensu.
KU KARANTA: 'Yan Boko Haram ba za su taba tuba ba - Ndume
Muhammad Ndume mai wakiltar yankin kudancin borno a majalisa ya bayyana wannan a lokacin da ya yi hira da wasu ‘yan jarida a Abuja a ranar Lahadi.
Sanata Ndume ya yi magana game da yadda gwamnatin tarayya ta ke kokarin kawo karshen rikicin Boko Haram, ya yi tir da afuwar da ake yi wa tsofaffin ‘yan ta’adda.
Ndume ya shawarci gwamnatin kasar ta canza salon rawarta. A cewarsa, ‘Mafi yawan ‘Yan Najeriya ba su goyon bayan yadda ake aikin operation safe corridor.”
Sanata Ali Ndume ya ce: “Ba daidai ba ne ka yi wa ‘yan ta’addan da su ka tuba afuwa a lokacin da ake tsakiyar yaki, ba a kai ga hangen samun nasara ba.”
KU KARANTA: 'Yan Boko Haram sun kashe mutane 75 a dare daya - Sanata
“Dole sai an gama yaki sannan za mu fara wannan.”
“Sojoji za su iya bada dama, a kyale kowa ya shigo, a dauke su, a ajiyesu a wani wuri a matsayin wadanda aka yi nasara a kansu wurin yaki, sai a horas da su.”
‘Dan majalisar ya cigaba da cewa: “Bayan yaki, za a yi shawo kansu da wadanda su ka yi wa ta’adi da mummunan aikinsu.”
“Haka ake yi a ko ina a Duniya.” Amma Ndume ya na ganin tsarin da aka dauko na yi wa Boko Haram afuwa ba tare da an ba wadanda su ka yi wa barna hakuri ba, bai dace ba.
“Wannan ba zai kawo zaman lafiyan da ake so ba.”
A baya kun ji yadda Ali Ndume ya nemi a yi bincike kan harin da yan ta’adda su ka kai Auno
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng