Kwamishinar Kaduna ta yi karin haske game da kudin kula da masu COVID-19
- Gwamnatin Kaduna ta bayyana yadda kudin jinyar COVID-19 ta ke tafiya
- Malam Nasir El-Rufai ne ya yi bayani ke-da-ke-ke a shafinsa na Facebook
Gwamnatin jihar Kaduna ta fito ta yi bayani daki-daki na duk kudin da ake kashewa wadanda su ka kamu da cutar COVID-19, har su kammala jinya a gadon asibiti.
Hakan na zuwa ne bayan wasu sun fara nuna rashin yarda game da maganar da gwamna Nasir El-Rufai ya yi, na cewa ana kashewa duk maras lafiya N400, 000.
Mai girma Malam Nasir El-Rufai ya fito da wannan bayani a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi.
Kwamishinar lafiyar jihar Kaduna, Amina Mohammed-Baloni, ta sa hannu a wannan jawabi da ya tabbatar da yadda gwamnati ta ke kashe N430, 000 kan duk mai jinya.
Jawabin Dr. Amina Mohammed-Baloni ya ce gwamnati ta yi haka ne bayan surutan da jama’a su ka fara yi da jin labarin irin kudin da ake kashewa wajen jinyar wannan cutar.
KU KARANTA: COVID-19: Gwamnati ta tsare wadanda su ka biyo ta Kaduna
1. Kudin da ake kashewa kafin a kwantar da mutum a gadon asibiti (Kudin kayan gwaji – N20, 000, VTM – N800, kwalbar daukar majina – N200, sandar daukar majina – N650.)
= N21, 650
2. Rigunan PPE
= N2, 400
3. Abinci
= N24, 000
4. Daukar maras lafiya zuwa wajen jinya
= N3, 500
5. Magungunan taimakawa mai COVID-19
= N 6, 000
6. Magungunan da ake sha idan abu ya cabe
= N 6, 000
7. PPE
= N 48, 000
8. Kudin wanki, sukola, lantarki, kayan aiki, da sauransu
= N 77, 000
KU KARANTA: COVID-19: Za mu iya sake rufe Kaduna idan... - El -Rufai
9. Gwaje-gwaje (wanda ake yi daga baya)
= N43, 300
10. Kudin da ake kashewa wajen neman wadanda aka yi hulda da su
= N3, 500
11. Kudin yi wa wadanda aka yi hulda da su gwaji (mutum 5)
= N108, 250
12. Sallama (Sa wa maras lafiya ido na kwanaki 14)
13. Dakunan jinya (Kudin gyara, na’urori da kayan aiki) a Kakuri, Kafanchan da Zariya
=N45, 221
14. Kudin abin da ba a rasa ba (Watan Mayu da Yuni)
= N47, 636
Adadin kudi: N436, 457
Kwanaki kun ji yadda wani jariri da ya kamu da COVID-19 a Kaduna ya warke.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng