Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

- Tsohon gwamnan jihar Adamawa a karkashin jam'iyyar PDP, Mista James Ngillari ya koma jam'iyyar PDP

- Shugaban jam'iyyar APC na jihar Adamawa, Alhaji Ibrahim Bilal ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Yola

- Mista Ngillari da ya sauya shekar tare da dubban magoya bayansa ya ce ba neman mukami yasa ya koma APC ba sai dai don samun 'yanci na siyasa

Tsohon gwamnan jihar Adamawa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, Mista James Ngillari, ya fice daga PDP ya koma jam'iyyar All Progressives Congress (APC).

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Adamawa, Alh. Ibrahim Bilal, ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar a garin Yola kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Adamawa: Tsohon gwamnan PDP, Ngillari ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC. Hoto daga The Nation
Source: Twitter

Bilal ya yi bayanin cewa tsohon gwamnan na PDP ya bar jam'iyyar ne tare da dubban magoya bayansa.

DUBA WANNAN: Sun mayar da mu karuwai, ga horo da yunwa: Yar Najeriya da aka ceto daga Libya

"Ina son amfani da wannan damar in sanar da cewa tsohon gwamnan jihar Adamawa karkashin jam'iyyar PDP, Mista James Ngillari ya koma jam'iyyar All Progressive Congress.

"Ngillari ya koma APC tare da dubban magoya bayansa bayan ya dauki lokaci mai tsawo yana shawarwari tare da dubban magoya bayansa.

"Ya shaida min baki da baki cewa ba ya dawo APC bane domin yana neman wani mukami amma domin ya samun yancin siyasa," in ji Bilal.

KU KARANTA: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Shugaban jam'iyyar na APC ya ce jam'iyyar a matakin kasa na jiha tana shirye shiryen maraba da tsohon gwamnan na PDP a hukumance nan ba da dadewa ba.

Ya ce jam'iyyar a matakin jiha tana aiki tare da kwamitin Mai Mala domin karfafa jam'iyyar gabanin babban zaben shekarar 2023 na kasa kamar yadda kamfanin dillancin labarai ta kasa, NAN, ta ruwaito.

A wani rahoton, kun ji cewa wani bakanike da ke Lafia a jihar Nasarawa, John Simon, ya batar da motar kwatomansa a yayin da ya shiga gidan wasu karuwai a sabon yankin Nyanya.

City Round ta gano cewa, Simon na tsaka da shakatawarsa da wata karuwa mai suna Stella Emeerga yayin da wasu mutane uku suka hada kai da ita wurin sace motar kirar Toyota Camry.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel