Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun samu nasarar bindiga kasurgumin dan bindiga Bobisky

Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun samu nasarar bindiga kasurgumin dan bindiga Bobisky

- Bayan kisan Terwase Gana a Benue, an sake samun nasarar kashe wani shahrarren dan bindiga

- Jami'an yan sanda sun bindiga Bobisky ne a jiharsa ta Rivers

- Gabanin kisansa, gwamnati tana nemansa ruwa a jallo

Wani kasurgumin dan fashi kuma mai garkuwa da mutane da ya addabi jihar Rivers, Honest Digbara wanda aka fi sani da Bobisky, ya gamu da ajalinsa hannun jami'an hukumar yan sanda.

An bindige dan bindigan wanda aka dade ana nema ruwa a jallo ne ranar Asabar.

Al'ummar jihar sun shiga murna da farin ciki yayinda suka samu labarin mutuwan Bobisky.

Gabanin samun nasarar hallakashi, gwamnati ta yi alkawarin kudi milyan 30 ga duk wanda ya ke da labarin inda dan bindiga yake.

An damke shine a wani harin bazata da hukumar yan sandan Rivers ta kai garin Korokoro dake karamar hukumar Tai ta jihar.

Bobisky ya dade yana ta'asa a sassan jihar kafin gamuwa da ajalinsa.

KU KARANTA WANNAN: Yari makaryaci ne, ban zabawa Matawalle kwamishanoni ba - Marafa

Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun samu nasarar bindiga kasurgumin dan bindiga Bobisky
Yanzu-yanzu: Jami'an tsaro sun samu nasarar bindiga kasurgumin dan bindiga Bobisky
Asali: Twitter

DUBA NAN: An yi garkuwa da Alkalan kotun Shari'ar Musulunci biyu a Najeriya

Kisan Bobisky ya biyo bayan hallaka dan bindigan da aka dade ana nema ruwa a jallo, Terwase Agwaza Gana,da jami'an Sojin 'Special forces' a jihar Benue sukayi.

Kwamandan 4 Special Forces Command, Doma, jihar Nasarawa, Maj. -Gen. Moundhey Ali, ya bayyanawa manema labarai ranar Laraba cewa an kashe Gana ne a hanyar Gbese-Gboko-Makurdi bayan musayar wuta.

Yace, "Misalin karfe 12:00 na ranar Talata, mun samu labarin shahrarren dan bindiga Terwase Akwaza Agbadu wanda aka fi sani da Gana na hanyar Gbese-Gboko-Makurdi.

"Dakarun rundunar Operation ‘Ayem Akpatuma III’ suka bazama tare hanyar."

"Misalin karfe 13:00, an yi musayar wuta tsakanin Soji da Gana inda aka kasheshi."

Kwamandan ya ce an damke yaran aikinsa 40 da manyan makamai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel