Hajj 2021: NAHCON ta fara yi wa maniyyata aikin hajji rajista a bana

Hajj 2021: NAHCON ta fara yi wa maniyyata aikin hajji rajista a bana

- Hukumar Kula da aikin Hajji na ƙasa, NAHCON, ta sanar da fara yi wa maniyyatan 2021 rajista

- Hukumar ta ce za a fara yi wa maniyyatan da suka bar kudinsu da hukumar tun bara kafin sabbin

- NAHCON ta shawarci hukumomin kula da maniyyata na jihohi su bi dokokin da aka gindaya musu yayin rajistan

Hajj 2021: NAHCON ta fara yi wa maniyyata rajista a bana
Hajj 2021: NAHCON ta fara yi wa maniyyata rajista a bana. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya ta buƙaci hukumomin kula da jin dadin alhazzai na jihohi su fara yin rajistan maniyyata hajji na shekarar 2021.

DUBA WANNAN: Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse

Kwamishinan NAHCON mai kula da ayyuka, Abdullahi Magaji Harɗawa cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce hukumomin Kula da aikin hajji na Saudiyya ne za su gindaya sharrudan yin aikin hajjin.

Ya kuma shawarci hukumomin kula da jin daɗin alhazzan su bi dokokin da za a gindaya musu yayin rajistan.

Ya tunatar da su cewa maniyyatan bara da suka bar kudinsu zuwa wannan shekarar ya kamata a fara yi wa rajista kafin sabbin mahajjatan wannan shekarar.

KU KARANTA: An kama wani mutum dauke da katin ATM 2,886 a filin jirgin sama zai tafi Dubai (Hotuna)

Ya ce shafin intanet na NAHCON zai kasance a bude awa 24 a kowanne rana domin maniyyatan su yi rajista kafin ranar da za a rufe rajistan.

A wani rahoton daban kun ji cewa a ƙalla katon ɗin taliya indomie guda 1,958 cikin 3,850 da ya kamata a raba wa mutane a matsayin tallafi a jihar Benue ne yan sanda suka gano an sayar da su a Kano.

Yan sanda sun yi nasarar kama wadanda ke da hannu wurin karkatar da kayan tallafin, an kuma yi holen su tare da wasu da ake zargi da aikata wasu laifukan a ofishin ƴan sanda ta Bompai.

An ƙiyasta cewa kuɗin talliyar da aka karkatar mai laƙabain "CA-COVID-19" ya kai Naira miliyan 4,411,800.

An gano talliyar ne a fitaccen kasuwar Singer da ke Kano kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164