Wata sabuwa: Matar mataimakin gwamna na zargin Adams Oshiomhole da yi mata barazanar kisa

Wata sabuwa: Matar mataimakin gwamna na zargin Adams Oshiomhole da yi mata barazanar kisa

- Matar mataimakin gwamna ta zargi Adams Oshiomhole da yi mata barazanar kisa

- Ta ce ya sanya 'yan daba suna lura da ita a duk inda ta sanya kafa a jihar su ta Edo

- Mai taimakawa gwamnan a fannin sadarwa, ya bayyana cewa kokari ne kawai suke na kawar yadda sunansu ya baci a jihar

Matar mataimakin gwamnan jihar Edo, Mrs. Maryann Shaibu ta koka akan barazanar kisa da tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Comrade Adams Oshiomhole yake yi mata.

A wata kara da Shaibu ta fitar ta hannun lauyoyinta masu kamfanin Idemudia Ilueminosen & Co, zuwa ga kwamishinan 'yan sandan jihar Lawan Jimeta, ta zargi Oshiomhole da cewa ba wai iya barazanar maganinta yake yi ba, ta bayyana cewa Oshiomhole ya tura 'yan daba su dinga lura da ita a karamar hukumar Etsako.

Wata sabuwa: Matar mataimakin gwamna na zargin Adams Oshiomhole da yi mata barazanar kisa
Matar mataimakin gwamnan Edo na zargin Adams Oshiomhole da yi mata barazanar kisa | Source: Facebook
Source: Facebook

Ta bukaci rundunar 'yan sandan ta gabatar da bincike akan wannan barazana da ake yi mata, ta kuma gabatar da hukunci akan Oshiomhole da mutanen shi da suke kokarin cutar da ita.

Sai dai kuma, Oshiomhole ta bakin mai taimaka masa a fannin sadarwa, Victor Oshioke, ya bayyana wannan kara da matar Shaibu ta shigar a matsayin kanzon kurege, da kuma kokarin daukar hankalin 'yan Najeriya akan bidiyon Mrs. Shaibu da yake ta yawo a shafukan sadarwa da take barazanar dukan wata tsohuwa da ta kusa yin sa'ar mahaifiyarta.

KU KARANTA: Kana taka Allah na tashi: Ango ya mutu kwanaki kadan bayan ya auri kyakkyawar amaryar shi

Oshioke ya ce: "Wannan kara shiri ne kawai na kokarin batawa Comrade Oshiomhole suna. Shaibu da matarsa su nemi wata hanya ta daban domin gyara sunan danginsu, wanda tuni ya riga ya baci akan abubuwan da suka yi da kuma bidiyon da aka dauka na barazanar da suke yiwa mutanen jihar Edo.

"Comrade Oshiomhole mutum ne mai son zaman lafiya ga kanshi dama mutanen da suke zaune da shi. Hankalin shi ya karkata ga tallata dan takarar gwamnan jam'iyyar APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu, da kuma abubuwan cigaba da zai kawowa mutanen jihar Edo, domin cigaban su."

KU KARANTA: Sai muna kwance ni da ita sai ta sulale zuwa dakin wani gardi suyi iskanci - Malamin Islamiyya ya kai matar shi kara kotu

Wani rahoto da Legit.ng ta kawo ya nuna yadda wasu magoya bayan jam'iyyar APC tare da hadin guiwar jami'an hukumar Hisbah ta jihar Yobe, suka ragargaza shagunan wasu 'yan kasuwa, wadanda suka sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a garinsu Gwamna Mai Mala Buni.

Wannan ragargazar ta faru ne kasa da sa'o'i 24 bayan 'yan kasuwar sun koma jam'iyyar PDP daga APC.

Wani ganau ba jiyau ba, ya sanar da Sahara Reporters cewa 'yan sandan Hisbah sun bada babbar gudumawa wurin ragargaza shagunan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel