Yadda 'yan sanda suka azabtar da budurwa mai shekaru 20 har ta mutu

Yadda 'yan sanda suka azabtar da budurwa mai shekaru 20 har ta mutu

- Wani dan sanda a jihar Nasarawa mai suna Alpha Lamurde ya zama abun zargi bayan da ya zabtar da wata budurwa har ta mutu

- Kamar yadda kanin budurwar mai suna Bilkisu Ummi Isa ya sanar, ya ce 'yan sandan sun kama ta ne bayan da saurayinta yayi sata

- Ana zargin saurayinta da satar kudi har miliyan 1.4 daga ubangidansa mai siyar da motoci a Abuja

Ana zargin wani dan sanda mai suna Alpha Lamurde da azabtar da wata budurwa mai suna Bilkisu Ummi Isa mai shekaru 20 a duniya, har ta mutu.

Lamarin ya faru a ofishin 'yan sanda da ke kusa da titin Calvary a Maraba, karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, Daily Trust ta wallafa.

An zargi 'yan sandan da azabtar da Ummi na tsawon kwana daya, kuma sun bada belinta bayan da suka ga ta fara aman jini a ranar Lahadi.

Dan uwanta mai suna Zakariya Isa, ya ce an zargi tsohon saurayinta mai suna Abdul da satar kudi har miliyan 1.4 daga wani ubangidansa mai siyar da motoci a Abuja.

Ya ce, abokin Abdul ne ya kira sunanta da yaji matsar 'yan sanda, lamarin da yasa suka kama ta.

Zakariya Isa yace 'yan sanda sun kamata suka dinga dukanta, kuma suna buga kanta da bango. Daga bisani sun kira iyayenta da suka ga tana ta suma.

KU KARANTA: Bidiyon wani yaro da yake yiwa mahaifiyarshi bayanin yadda ya kamu da son wata budurwa ya bawa mutane mamaki

Yadda 'yan sanda suka azabtar da budurwa mai shekaru 20 har ta mutu
Yadda 'yan sanda suka azabtar da budurwa mai shekaru 20 har ta mutu. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

Amma kamar yadda kawar marigayiyar mai suna Rukayya Muhammad ta sanar, "wani matashi mai suna Jibrin ne aka sa ya nemo Abdul. Da ya kasa samunsa, sai ya kai 'yan sandan wurin budurwarsa.

"Sifetan dan sanda ya dinga marinta da dukanta. Amma ya bani lambar wayarsa a kan cewa yana sona. Hakazalika bai duke ni saboda yana so mu hadu a wani otal. Lambar wayarsa ita ce 07065743117.

"Da na duba a wata manhaja sai na ga sunansa Alpha Lamurde kuma na dauko hotonsa daga WhatsApp.

"A lokacin da nace musu tana suma, sai ya watsa mata ruwa. An kama mu sannan aka bada belinmu a ranar Litinin. Bilkisu ta rasu a ranar Lahadi," Rukayya tace.

A yayin da aka tuntubi rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa, sun ce dama can Bilkisu tana da wani ciwo. Ba dukan 'yan sanda bane ya kasheta.

KU KARANTA: An kama mutane biyu da suka kaiwa Hausawa hari a jihar Rivers

A wani labari na daban, hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna, ta ce an saka ranar jarabawar shiga makarantar horon hafsin 'yan sanda da ke Wudil a jihar Kano domin diban dalibai karo na takwas.

An saka za a yi jarabawar a ranar Alhamis, 17 ga watan Satumban 2020 a dukkan fadin kasar nan, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya bayyana haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis a garin Kaduna.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel