Mijina ba ya daukata a bakin komai - Uwar gida ta roki kotu ta raba aurensu
- Wata matar aure, Misis Blessing Etim ta roki kotu ta raba auranta da mijinta
- Etim ta yi zargin cewa ko kashi ya fi ta daraja a wajen angon nata
- Sai dai alkalin kotun ya dage sauraron shari’an saboda rashin bayyanan wanda ake kara a gabansa
Wata ma’aikaciyar gwamnati mai suna Misis Blessing Etim, a ranar Alhamis, ta maka mijinta a gaban kotu a Jikwoyi domin neman a raba auransu.
Matar ta nemi a raba auren ne bisa hujjar cewa mijin nata baya ganinta da gashi domin ko kashi ya fi ta daraja.
Etim, wacce ke zama a jihar Nasarawa, ta yi wannan zargi ne a cikin takardar neman a raba aure da ta mika wa kotun.
“Na gaji da wannan aure. Tun da na auri mijina ban san kwanciyar hankali ba. A koda yaushe fada yake yi da ni. Abu mafi muni shine yana cin zarafina a gaban yan uwa da jama’ar gari.
“Yana dauka ta kamar tsumman kashi,” ta yi zargi.
KU KARANTA KUMA: Na san yadda APC, PDP, da sauransu suke zabar shugabanninsu na kasa, in ji Yari
Mai karar ta fada ma kotu cewa akwai lokacin da mijinta ya so murkushe ta, “cewa idan ba don makwabta da suka zo suka ceceni ba, da na dade da mutuwa.”
Ta kuma yi zargin cewa mijinta ya daina kula da dawainiyar iyalinsa “ni ce ke biyan kudin hayar gidanmu, kudin magani, ci da sha hatta da kudin makarantar yara, ba zan iya ci gaba da wannan auren ba.”
Wanda ake karan bai bayyana a kotu ba kuma bai aiko kowani takarda na dalilin rashin zuwansa ba.
KU KARANTA KUMA: Jihar Bauchi: Wani babban jigo a PDP ya koma APC, ya bi sahun Dogara
Alkalin kotun, Jemilu Jega, a hukuncinsa ya ce: “wanda ake karan bai bayyana a kotu ba kuma bai aiko kowani dalili ba. Saboda haka, don yin adalci, za a lika takardar kotu a gidan wanda ake karan.”
Jega ya dage sauraron lamarin zuwa 15 ga watan Satumba don ci gaba da shari’a.
A wani labarin, mun ji cewa uwargidar gwamnan jihar Kwara, Misis Olufolake Abdulrazaq, ta hayar muhalli ga Risikat, mace mai launin ido tamkar na mage, wacce aka sake daura auranta da mijinta da ya guje ta, Abdulwasiu Omodada.
Sakataren labarai na uwargidar gwamnan, Yinka Adeniyi, ya ce Olufolake, ta shirinta mai zaman kansa, Ajike Support Group, ta sama wa ma’auratan muhalli mai dakuna biyu a birnin Ilorin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng