Hukumar kwastam ta samu fiye da biliyan ₦9 a cikin wata 8
> Hukumar kwastam ta samu kudin shiga da yawansu ya kai biliyan ₦976.6 daga watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2020.
> Tiriliyan ₦1.3 hukumar kwastam ta samu a matsayin kudin shiga a shekarar 2019
> Masanin tattalin arziki, Promise Amahah, ya yabawa hukumar kwastam a kan samun damar tattara adadin kudaden duk da barkewar annobar korona
Hukumar hana fasa kwauri ta kasa wacce aka fi sani da 'Kwastam' ta samu rabanu na biliyan ₦976.6 daga watan Janairu zuwa Agusta na shekarar 2020.
A wata takarda da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya wallafa ranar Alhamis, an nuna cewa an samu kudaden ne daga rabanu a kan kayan da aka shigo dasu Najeriya da kudin duti da sauransu.
NAN ta bayyana cewa takardar ta fito ne daga ofishin hulda da jama'a na hukumar kwastam.
Kididdiga ta nuna cewa kudaden da hukumar Kwastam ta samu daga rabanu a kan kayan da aka shigo dasu basu taba kaiwa yawan na wannan karon ba.
Alkaluma sun nuna cewa kudaden haraji da aka kara a kan kaya (VAT) sune ke bin bayan yawan kudin da hukumar ta samu daga rabanu a kan shigo da kaya.
Jimillar biliyan N471.7 hukumar kwastam ta samu a matsayin rabanu daga kayan da aka shigo dasu Najeriya.
Kazalika, hukumar kwastam ta samu jimillar biliyan N216 daga VAT.
An samu wasu kudaden; biliyan N120.4 da biliyan N84.3 daga wasu bangarorin daban.
KARANTA: Rashin tsaro: Fiye da Katsinawa 2,226 sun yi hijira zuwa Gombe
KARANTA: Farfado da tattalin arziki: Buhari ya umarci a sakarwa 'yan Najeriya tiriliyan ₦2.3
An karbi biliyan N6.6 a matsayin rabanu daga kananan harkoki da kuma biliyan N76.9 da aka samu daga biyan duti.
Tiriliyan ₦1.3 hukumar kwastam ta samu a matsayin kudin shiga a shekarar 2019 da ta gabata.
Wani masanin tattalin arziki, Promise Amahah, ya yabawa hukumar kwastam a kan samun damar tattara kudaden duk da bullar annobar korona a fadin duniya.
Mista Amahah ya bayyana cewa, babu shakka zuwa karshen wannan shekarar, hukumar kwastam za ta iya samun kudaden da suka zarce na shekarar 2019.
NAN ta wallafa cewa shugaban hukumar kwastam na kasa, Hameed Ali, ya bayar da tabbacin samun isassun kudin shiga duk da annobar korona.
"Annobar korona ta girgiza tattalin arzikin Najeriya da sauran kasashen duniya, amma duk da haka zamu yi kokarinmu wajen samar da wadatattun kudin shiga," a cewar Ali.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng