PDP ta zabga babbar asara a jihar Bauchi, jigonta ya bi Dogara APC
Tsohon dan majalisar wakilai, Salisu Ningi, ya bar jam'iyyar PDP a jihar Bauchi. Ya garzaya domin hadewa da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, wanda ya kwatanta da madubin dubawarsa na siyasa.
Ningi wanda ya wakilci mazabar Ningi da Warji a tarayya, ya sanar da hakan ta wata wasikar barin jam'iyyar da ya aike wa shugaban jam'iyyar PDP na gundumar Ningi ta yamma.
A wasikar mai kwanan 6 ga Satumban 2020, Ningi ya ce shi da mabiyansa ba za su iya ci gaba da zama a jam'iyyar PDP ba domin tuni suke ganin gazawarta.
Takardar ta ce, "Idan za ku tuna, a yayin zaben 2019 na shugaban kasa, babban dan siyasar jiharmu, Yakubu Dogara ya koma jam'iyyar PDP saboda ya tsere wa mulkin kama-karya na M.A Abubakar.
"Wanda a haka aka yi nasara Sanata Bala Abdulkadir Muhammad ya haye kujerar shugabancin. Amma sai muka gane cewa, abinda ya koremu daga jam'iyyar a baya, shine ke ci gaba da faruwa an ki gyarawa."
KU KARANTA: Matashi ya kashe mahaifiyarsa a kan ruwan lemo da kuma motarta

Source: Twitter
KU KARANTA: Karin farashin man fetur: Jama'ar Kaduna sun koka da ninkuwar kudin mota
Idan za mu tuna, tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya yi bayani a kan dalilin da yasa ya bar babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya koma jam'iyyar APC.
A ranar Juma'a, jaridar Premium Times ta ruwaito yadda Dogara ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari bayan komawarsa jam'iyyar mai mulki.
A wasikar barin PDP da Dogara ya mika ga shugaban jam'iyyar na unguwar Bagoro, mai kwanan wata 24 ga Yulin 2020, ya ce rushewar shugabanci a jiharsa karkashin mulkin Gwamna Bala Mohammed yasa ya bar jam'iyyar.
Tsohon kakakin ya ce ba zai yi nasarar tambaya ba a kan al'amura ba tare da an zarge shi da rashin biyayya ba in har zai ci gaba da zama a PDP.
Ya ce matukar zai yi watsi da dabi'ar fadin gaskiya ga shugabanni a jihar Bauchi, bayan wanda ya yi a zamanin mulkin Isa Yuguda da Mohammed Abubakar, zai zama mara akida a siyasar jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng