Osinbajo: Mataimakin Shugaban kasa ya bankado badakala a yarjejeniyar P & ID
Wani Alkalin Birtaniya, ya ce maza-mazan da Farfesa Yemi Osinbajo ya yi, ya taimaka wajen gano cuwa-cuwar da aka nemi a tafka a yarjejeniyar P & ID.
Alkali mai shari’a Ross Cranston a babban kotun Birtaniya, ya ce mataimakin shugaban kasar Najeriya ya bi diddiki, ya gano damfarar da aka shimfida a wannan yarjejeniya.
Sir Ross Cranston ya ce jawabin da Farfesa Yemi Osinbajo ya fitar mai taken “fraud on the nation” a 2018 a kan damfarar da ake neman yi wa Najeriya, ya yi tasiri sosai.
Jaridar Pulse ta fitar da wannan dogon rahoto a ranar 5 ga watan Satumba, 2020.
Alkalin ya ce Yemi Osinbajo ya fara bibiyar wannan yarjejeniya ne tun a shekarar 2017, bayan Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, ya sanar da shi halin da ake ciki.
KU KARANTA: Buhari ya sake fadawa Ministocinsa su nemi COS idan su na son ganinsa
Babban Alkalin ya ce: "Bayan wata zama da aka yi a ranar 13 ga watan Maris, 2017, Malami ya rubutawa mataimakin shugaban kasa takarda, a lokacin ya na shugaban rikon-kwarya.”
Ministan shari’an Najeriyar ya yi wa Farfesa Osinbajo bayanin halaye biyar da Najeriya za ta iya samun kanta, da kuma shawarwarin abin da ya kamata ayi a duk yadda ta kama.
Malami SAN ya fadawa Osinbajo cewa abin yi shi ne ayi sulhu da P & ID a wajen kotu, ko kuma a binciki ainihin yarjejeniyar da kamfanin ya shiga da Najeriya domin gano tuntube.
Tsakanin Afrilu da Mayun 2017, Mai girma Osinbajo ya yi na’am da zama ayi sulhu da kamfanin P & ID, a karshe shirin yin sulhu a wajen kotu da wannan kamfani bai yiwu ba.
KU KARANTA: Jawabin Shugaba Akufo-Addo na zama Shugaban ECOWAS
Kokarin da Osinbajo ya yi ya zarce na ikon da ya ke da shi a matsayin mukaddashin shugaban kasa, ya karbi maganar Ministan shari’a, kuma ya rubutawa Buhari takarda.
Ministan shari’a da na mai a lokacin sun nemi ayi sulhu, amma Osinbajo ya dauki lokaci na musamman, ya duba yarjejeniyar da kyau, ya ce ana neman a cuci gwamnatin tarayya.
A karshe wannan ya yi sanadiyya aka koma kotu, har ta kai Najeriya ta fara samun nasara a shari’ar da aka yanke na cewa gwamnatin kasar za ta biya P & ID tarar Dala biliyan 9.6.
Ku na da labari cewa an shiga yarjejeniya da P & ID ne a lokacin da Marigayi Ummaru ‘Yar’adua bai da lafiya, sa'ilin da Goodluck Jonathan ya ke mukaddashin shugaban kasa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng