Tirkashi: An dakatar da daurin aure bayan wani mutumi ya shiga wajen daurin aure yace shine mahaifin amarya da ango

Tirkashi: An dakatar da daurin aure bayan wani mutumi ya shiga wajen daurin aure yace shine mahaifin amarya da ango

- Mutumin da ya bayyana cewa masoyan 'ya'yanshi ne, ya ce ya bar 'ya'yan da mahaifiyarsu kafin su rabu

- Ya ce ya shafe shekaru 10 yana neman 'ya'yan shi, saboda yayi kokarin neman mahaifiyarsu ya kasa samun ta

- Mutumin ya ce matarshi ta gano yana kwanciya da wata, sai ta sa zamansu ya fara samun matsala, inda ta gudu da yaransu

An dakatar da daurin auren wasu masoya a Jihar River, bayan wani mutumi ya fito ya bayyana cewa shine mahaifin amaryar da angon, a yayin da ake shirin daura auren.

Anne Magwi da Jotham Munini, wadanda ya kamata a daura aurensu a ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, an ruwaito cewa iyayensu daya.

Sai dai kuma a wani rahoto da jaridar The Nation ta ruwaito, ya nuna yadda mahaifinsu tare da 'yan uwanshi suka isa wajen daurin auren, suka dakatar da daurin auren.

Tirkashi: An dakatar da daurin aure bayan wani mutumi ya shiga wajen daurin aure yace shine mahaifin amarya da ango
Hoton wajen bikin aure da aka dauka kafin 'yan biki su karaso | Photo Source: Facebook
Source: Depositphotos

A cewar Fasto Festus Muli, mutumin da ya bayyana cewa masoyan 'ya'yanshi ne ya samu sabani da mahaifiyar yaran kafin su rabu saboda wasu dalilai da dama.

KU KARANTA: Rikicin aure: Mun daidaita tsakanina da Muhammad Babangida, 'yar gidan biloniya, Rahma Indimi

"Daya daga cikin yaran, angon, sun haife shi ba ta hanyar aure ba," cewar Fasto Muli.

Faston ya ce, mutumin James Sidai, ya ce bayan matarshi ta gano cewa yana kwanciya da wata, sai zamansu ya zama rikici, hakan ya sanya ta kwashe 'ya'yan ta gudu da su.

Daga nan ne yayi kokarin cigaba da soyayya da tsohuwar masoyiyarshi, amma suma basu jima ba suka rabu saboda rashin kudi.

Mutumin ya bayyana cewa daya matar sun rabu da ciki na tsawon watanni hudu, inda daga baya ta auri wani malamin makaranta.

Sidai ya ce ya gabatar da hotunan yaran a lokacin suna yara da kuma lokacin da suke kwaleji, wadanda ya samu daga wajen abokanan shi da 'yan uwa da suka yi mu'amala da su.

KU KARANTA: Bidiyon wani yaro da yake yiwa mahaifiyarshi bayanin yadda ya kamu da son wata budurwa ya bawa mutane mamaki

Mutumin ya kwashe shekaru 10 yana neman yaran shi cikin wahala.

Dangane da macen kuwa, wani abokinshi sun sanar da shi cewa matar ta haifi yarinya mace wacce suke kama sosai da shi.

Hakan ya tilasta faston dakatawa da daurin auren, sannan ya kira iyayen domin suyi magana.

Angon, a cewar faston an sanar da shi cewa mahaifinsa ya mutu ta hanyar hatsarin mota, a lokacin da yake yaro, inda ita kuma macen ta taso ta san malamin makarantar da mahaifiyarta ta aura ne.

Domin gudun abin kunya faston ya bayyanawa 'yan coci cewa an daga daurin auren.

A wani labari kuwa, Legit.ng ta kawo muku yadda Rahama Indimi ta bayyana cewa ta daidaita da tsohon mijinta, Muhammed Babangida.

A shekarar 2016, labarai sun yadu cewa auren su da suka shafe shekaru 14 suna tare, tsakanin 'yar gidan fitaccen mai kudin nan Mohammed Indimi, da Muhammed dan gidan tsohon shugaban kasar mulkin soja, Ibrahim Babangida, ya rabu.

Duka su biyun sunyi ta shiga kotu tun lokacin kan rikicin wanda zai rike yaran.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel